Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Ahmed Aliyu a Zaben Gwamnan Sokoto
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tabbatar da nasarar da gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar
- Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Saidu Umar suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen
- Umar ya yi zargin cewa mataimakin gwamnan ya bayar da takardun bogi da tafka maguɗi a zaɓen, zargin da a cewar kotu ya kasa tabbatarwa a gabanta
Jihar Sokoto - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto, ta yi watsi da ƙarar da dan takarar jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar ya shigar gabanta kan nasarar da gwamna Ahmed Aliyu ya yi a zaɓen da aka yi ranar na 18 ga watan Maris, cewar rahoton Daily Trust.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana gwamna Ahmed Aliyu, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma Umar ya ƙalubalanci nasarar da ya samu bisa zargin mataimakinsa da gabatar da takardun bogi da tafka maguɗi a zaɓen.
Umar ya ƙalubalanci nasarar gwamna Aliyu
Ƙarar da ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP ya shigar dai tana ƙalubalantar nasarar gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da mataimakinsa Gobir.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saidu Umar ya yi zargin cewa gwamnan bai cika sharuɗɗan cancanta tsayawa takara ba, sannan ya kuma yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen gwamnan.
Wane hukunci kotu ta yanke
A hukuncin da ta yanke a ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Huruna Mshelia, ya ce mai shigar da ƙara ya kasa iya tabbatar da zargin da yake yi, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Kefas
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Taraba, ta tabbatar da nasarar da gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta Sani Yahaya suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen.
Asali: Legit.ng