An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin da Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Zaben Ogun
- An tsaurara matakan tsaro yayin da gwamnan jihar Ogun zai san makomarsa yau Asabar, 30 ga watan Satumba, 2023
- Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaron haɗin guiwa sun mamaye harabar Kotun tun da sanyin safe, sun toshe wasu tituna
- Jam'iyyar PDP da ɗan takararta ne suka kalubalanci nasarar gwamna Abiodun a zaben 18 ga watan Maris, 2023
Jihar Ogun -Jami’an tsaro na hadin gwiwa sun mamaye harabar kotun majistare da ke Isabo, Abeokuta, inda kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Ogun take zamanta.
Kwamitin alkalan Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Hamidu Kunaza zai yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Ladi Adebutu, suka shigar yau Asabar, 30 ga watan Satumba.
Masu shigar da ƙarar suna ƙalubalantar nasarar gwamna Dapo Abiodun na jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, Daily Trust ta rahoto.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro masu ɗumbin yawa sun mamaye harabar Kotun tun da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kulle hanyoyin da ke zuwa kotun Isabo domin hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa, yayin da aka girke wasu motocin yaki masu sulke guda biyu a gaban kotun.
An hana 'yan jarida shiga Kotun
Jami’an tsaron da suka kewaye wurin tamkar an yi ruwansu sun hana wasu ‘yan jarida shiga harabar kotun, kamar yadda This Day ta ruwaito.
Bayanai sun nuna cewa ana tsammanin Kotun zata fara zaman ƙarshe na yanke hukunci da misalin ƙarfe 9:00 na safiya.
Tun a baya dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Abiodun na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe bayan ya samu ƙuri'u 276,298.
Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, Adebutu, ya zo na biyu da ƙuri'u 262,380 yayin da Biyi Otegbeye na jam'iyyar ADC ya tashi da ƙuri'u 94,754 a matsayi na uku.
Sai dai PDP da Adebutu sun kai karar Abiodun da APC a gaban kotun, inda suka yi zargin cewa gwamnan bai samu rinjayen kuri’un da aka kada ba a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Gwamnan PDP Ya Soke Shagalin Bikin Ranar Samun 'Yancin Kan Najeriya
A.wani rahoton kuma Gwamna Adeleke na jihar Osun ya soke bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya wanda ya saba gudana ranar 1 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ya roƙi mazauna jihar da su yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng