NNPP Ta Rusa Kwamitin NWC Karkashin Abba Kawu Ali, Ta Amince Da Korar Kwankwaso

NNPP Ta Rusa Kwamitin NWC Karkashin Abba Kawu Ali, Ta Amince Da Korar Kwankwaso

  • Kwamitin amintattu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya gudanar da taronsa a ranar Juma'a 29 ga watan Satumba a jihar Lagas
  • A yayin taron, BoT ya rushe kwamitin NWC na jam'iyyar karkashin jagorancin Abba Kawu Ali
  • Haka kuma, NNPP ta amince tare da tabbatar da korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takararta na shugaban kasa a babban zaben 2023

Jihar Lagos - Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta amince da rushe kwamitin ayyuka na NWC karkashin jagorancin Abba Kawu Ali.

Kwamitin BoT ta kuma tabbatar da korar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwakwanso, rahoton Nigerian Tribune.

An tabbatar da korar Kwankwaso a taron BOT na NNPP
NNPP Ta Rusa Kwamitin NWC Karkashin Abba Kawu Ali, Ta Amince Da Korar Kwankwaso Hoto: NNPP
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron BoT na jam’iyyar NNPP wanda ya gudana a Otal din Rockview da ke Apapa, jihar Lagas a ranar Juma’a, 28 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

Ba za mu lamunci gyara a kundin tsarin mulkin jam'iyya ba sai bayan zaben 2027, NNPP

Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar na 2022 zai ci gaba da kasance yadda yake cewa ba za a yi la'akari da gyara shi ba har sai bayan babban zaben 2027.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren labaran jam'iyyar na kasa, Alhaji Abdulsalam Abdulrasaq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka gabatarwa manema labarai.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Kundin tsarin mulkin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na 2022 (Kamar yadda aka gyara) zai ci gaba da kasance kundin tsarin mulkin jam’iyyar kuma ba a amince da gyaran kundin tsarin mulki ba har sai bayan babban zaben 2027. Babban ofishin NNPP shine fili mai lamba 511, Herbert Macaulay Way, Willlands Plaza, Zone 4, Wuse Abuja.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Babban Kamu Yayin Da Mambobin PDP, Labour Dubu 50 Su Ka Sauya Sheka A Wata Jiha, Sun Yi Alkawari

"An rushe kwamitin ayyuka na jam'iyyar na kasa karkashin jagorancin Abba Kawu Ali wanda aka kafa ba tare da bin ka'ida ba kuma za a sanar da INEC ba tare da bata lokaci ba.
“An tabbatar tare da amincewa da korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP)."

Kungiyar Kwankwasiyya bata da hurumin ci wa jam'iyyar NNPP albasa

Kwamitin amintattun ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da taron manema labarai da ra'ayin kungiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan harkokin jam'iyyar da kuma hukuncin da kotun zaben gwamnan jihar Kano ta yanke, rahoton New Telegraph.

Ya kara da cewar:

"Kungiyoyi ne masu ra'ayi kawai wadanda suka yi amfani da inuwar jam'iyyar don babban aben 2023, amma kawancensu ya kare da zaben, kuma saboda haka kungiyoyin basu da hurumin yin magana da yawun jam'iyyar.
"Za a yi nazari a kan hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Kano da ta tsige dan takarar jam'iyyar, Gwamna Abba Yusuf a ranar Laraba, 20 ga watan Satumbar 2023, da niyan tunkarar kotun daukaka kara don neman gyara."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Barazana ga alkalai: Da gaske za a kama Kwankwaso? sabbin bayanai sun fito

A wani labarin, mun ji cewa gamayyar ƙungiyar yaƙi da ta'addanci (NCAT) ta yi kira da a kamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kungiyar ta ce tana kira da a damke Kwankwaso ne bisa zargin barazana ga rayuwar alƙalan da suka jagoranci shari'ar zaben gwamnan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng