Kaduna: Jam'iyyar PDP Ta Yi Watsi da Hukuncin Tabbatar da Nasarar Uba Sani
- Jam'iyyar PDP ba ta gamsu da hukuncin tabbatar da Malam Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna ba
- A wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na jihar ya fitar ranar Jumu'a, ya ce jam'iyyar ta yanke ɗaukaka ƙara zuwa gaba
- A jiya Alhamis, 28 ga watan Satumba Kotun zabe ta tabbatar da nasarar gwamna Uba Sani na APC a zaben 18 ga watan Maris
Jihar Kaduna - Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi fatali da hukuncin da Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar ta yanke ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa PDP ta nuna rashin amincewa da hukuncin wanda ya tabbatar da nasarar Malam Uba Sani na jam'iyyar APC a zaben watan Maris, 2023.
Babbar jam'iyyar adawan ta bayyana cewa zata ƙalubalanci wannan hukunci a Kotun ɗaukaka ƙara domin ta kwato nasarar ɗan takararta da aka ƙwace.
Mai magana da yawun jam'iyyar PDP ta Kaduna, Alberah Catoh, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Jumu'a a cikin birnin Kaduna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Catoh ya ce bayan nazarin da Lauyoyi suka yi jiya da daddare, sun gano cewa hukuncin da Alƙalan Kotun suka yanke bai cika ka'idojin adalci ba.
Wannan martani na jam'iyyar PDP na zuwa ne awanni 24 bayan Kotun zaɓe mai zama a Kaduna ta tabbatar da nasarar APC bayan ta kori ƙarar Isa Ashiru Kudan.
Hukuncin ya saɓa wa dokokin zaɓe - PDP
Kakakin jam'iyyar PDP ya ƙara da cewa hukuncin da Kotun ta yanke bai dace da dokoki, ka’idoji da sharuɗɗan kundin dokokin zaben Najeriya ba.
A rahoton The Cable, Catoh ya ce:
“Saboda haka jam’iyyarmu ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja, a cikin wa’adin da doka ta kayyade."
Catoh ya kuma bukaci magoya bayan PDP da ke fadin jihar da su kwantar da hankulan su tare da yin imani da cewa duk nisan jifa kasa zai faɗo.
Kotun Zaɓe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP
A wani rahoton kuma Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zama a jihar Delta ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwor na jam'iyyar PDP
Kwamitin kotun karkashin jagorancin Mai shari'a C.H. Ahuchaogu, ya kori karar da APC da dan takararta, Sanata Ovie Omo-Agege suka shigar don kalubalantar nasarar Oborevwor.
Asali: Legit.ng