Barazana Ga Alkalai: Da Gaske Za a Kama Kwankwaso? Sabbin Bayanai Sun Fito

Barazana Ga Alkalai: Da Gaske Za a Kama Kwankwaso? Sabbin Bayanai Sun Fito

  • An gargaɗi Sanata Rabiu Kwankwaso da mabiyansa 'yan Kwankwasiyya su canja halayensu na neman rigima da tada zaune tsaye
  • Wannan ya biyo bayan hukuncin da Alkalai uku na Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano suka yanke
  • Wata ƙungiyar yaƙi da ta'addanci a Najeriya ta yi kira da a kama Sanata Kwankwaso bisa zargin yi wa alƙalai barazana

Gamayyar ƙungiyar yaƙi da ta'addanci (NCAT) ta yi kira da a kamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kungiyar ta ce tana kira da a damke Kwankwaso ne bisa zargin barazana ga rayuwar alƙalan da suka jagoranci shari'ar zaben gwamnan jihar Kano.

Kwankwaso tare da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Barazana Ga Alkalai: Da Gaske Za a Kama Kwankwaso? Sabbin Bayanai Sun Fito Hoto: NNPP
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da ƙungiyar NCAT ta aiko wa jaridar Legit Hausa ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Yi Murnar Ranar Samun 'Yancin Kai Ba" Gwamnan APC a Arewa Ya Bayyana Dalilai

A sanarwan, shugaban NCAT na ƙasa, Kwamared Terrence Kuanum, ya yi gargadin cewa akwai bukatar a dakile wuce gona da iri da 'yan Kwankwasiyya ke yi ba tare an taka musu birki ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa Najeriya na iya fuskantar wani sabon tashin hankali idan har ba a shawon kan munanan ɗabi'un ‘yan Kwankwasiyya a kan lokaci ba.

Kuanum ya ce:

"Kowa ya san halin da Zamfara ke ciki a halin yanzu, idan aka bar waɗan nan mutane suna wuce gona da iri da cin mutuncin alƙalai kusan kullum kuma gwamnatin Kano na basu kariya to akwai matsala."
"Farko muna buƙatar ɗaukar matakan tsare alƙalai musamman na Kotun ɗaukaka ƙara da gidajen da suke zama musamman waɗanda ke zaune a cikin jihar Kano."

NCAT ta buƙaci mahukunta sun damƙe Kwankwaso

Yayin da take jinjina ga shugaban alƙalan Najeriya bisa ƙara wa alkalan da ke jagorantar shari'o'in zabe kwarin guiwa, ƙungiyar ta ce matakin ya yi daidai da tsarin demokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

"Bamu Yarda Ba" Jam'iyyar PDP Ta Fusata Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC

Daga nan kuma NCAT ta yi kira ga Sufetan 'yan sanda na ƙasa ya gaggauta bada umarnin kamo jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya domin a titsiye shi kan barazana ga rayuwa da zaman lafiyar Kano.

"Ba Zaka Iya Kai Tinubu Ga Nasara Ba a 2027" Kwankwaso Ya Caccaki Ganduje

A wani rahoton na daban Sanata Rabiu Kwankwaso ya maida zazzafan martani ga Ganduje kan kalaman da ya yi cewa shi babban mara nasara ne.

Jagoran NNPP na ƙasa ya yi ikirarin cewa Ganduje ba zai kai shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ga tudun nasara ba a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262