Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar Jam'iyyar APC a Jihar Ondo

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar Jam'iyyar APC a Jihar Ondo

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun jihar Ondo ta soke nasarar ɗan majalisar jam'iyyar APC a jihar
  • Kotun ta bayyana zaɓen Hon. Nelson Akinsuroju mai wakiltar mazaɓar Ile-Oluji/Okeigbo a matsayin wanda bai kammalu ba
  • A hukuncin da kotun ta yanke, ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sake zaɓe a wasu rumfunan zaɓe shida na mazaɓar

Jihar Ondo - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun jihar Ondo da ke zamanta a Akure ta soke zaɓen ɗan majalisar dokokin jihar Ondo mai wakiltar mazabar Ileoluji/Okeigbo, Hon. Nelson Akinsuroju na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Yayin da take yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP), Babatunde Fadare ya shigar kan zaɓen Akinsuroju, kotun ta bayyana cewa zaben da aka yi a mazaɓar Ile-Oluji/Okeigbo a ranar 18 ga Maris, 2023, bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC a Jihar Arewa

Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Ondo
Kotu ta kwace nasarar dan majalisar jam'iyyar APC a jihar Ondo Hoto: Nelson Akinsuroju
Asali: Facebook

Wane umarni kotun ta bayar?

Don haka ta ba da umarnin sake gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe shida daga cikin rumfunan zabe 27 da ɗan takarar PDP ke ƙalubalanta, daga cikin rumfunan zaɓe 191 da ke mazabar, cewar rahoton Vanguard.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun mai alƙalai uku wacce ke ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Rose Soji, yayin da yake yanke hukunci, ya bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zaɓe shida da abin ya shafa a karamar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo ta jihar Ondo.

INEC ta bayyana Akinsuroju, a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 10,207, inda ya doke ɗan takarar PDP wanda ya samu ƙuri’u 9,287.

Sai dai, Fadare ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen bisa hujjar cewa zaben bai inganta ba saboda rashin bin dokokin zabe, kuma Nelson Akinsuroju bai samu ƙuri'u mafiya yawa ba a zaɓen.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Jam'iyyar ADC Bisa Nasarar Gwamnan Jihar Gombe

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan APC

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Gombe, ta tabbatar da nasarar gwamna Inuwa Ƴahaya na jam'iyyar APC, a zaɓen gwamnan jihar.

Kotun ta yi fatali da ƙararrakin da jam'iyyun ADC da PDP suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen da aka gudanar na ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng