Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Inuwa Yahaya Na Jam'iyyar APC
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Gombe ta tabbatar da sahihancin zaɓen gwamna Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC
- Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta suka shigar saboda rashin cancanta
- Jam'iyyar PDP da Mohammed Barde sun ƙalubalanci nasarar gwamna Inuwa a gaban kotun bisa zargin tafka maguɗi a zaɓen na ranar 18 ga watan Maris
Jihar Gombe - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Gombe ta tabbatar da nasarar gwamna Inuwa Yahaya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris 2023.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa kotun a ranar Talata, 26 ga watan Satumban 2023, ta yi watsi da ƙarar da jamviyyar PDP da ɗan takararta, Mohammed Barde, suka shigar domin ƙalubalantar nasarar da gwamna Inuwa Yahaya ya samu a zaɓen.
Meyasa kotun ta yi fatali da ƙarar?
Kotun zaɓen mai alƙalai uku wacce mai shari’a S.B Belgore ke jagoranta, ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barde ya yi zargin cewa zaɓen da aka gudanar wanda ya samar da gwamna Inuwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, cike yake da kura-kurai da dama ciki har da sayen ƙuri'u.
Jam'iyyar PDP ta kuma yi zargin cewa ba a zaɓi gwamna Inuwa Yahaya da mafo yawan ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen ba.
Sai dai kotun ta ce zargin ba shi da tushe ballantan makama, kuma masu shigar da ƙarar sun kasa tabbatar da magudin zabe da suke zargin an aikata, saboda haka sai suka yi watsi da ƙarar, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Tun da farko kotun ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar ADC ta shigar tana ƙalubalantar nasarar gwamna Inuwa Yahaya, inda ta ce jam'iyyar ta kasa kawo ƙwararan hujjoji.
Tabbas Inuwa ya ci zaɓe
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Gombe mai suna Sani Musa, wanda ya nuna gamsuwarsa kan wannan hukuncin da kotun ta yanke.
Malam Sani ya bayyana cewa tabbas gwamna Inuwa ne ya lashe zaɓe domin jam'iyyun adawa ba su da ƙarfi a Gombe, kuma an yi amfani da kuɗi wajen siyan ƙuri'u.
Ya ƙara da cewa hatta wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP, an ba su kuɗi domin kada su je wajen zaɓen.
Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Otu
A wani labarin kuma, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kuros Riba ta kori karar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Sandy Onor, suka shigar gabanta.
Kotun ta tabbatar da nasarar gwamna Bassey Otu na jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng