Kotun Zabe Ta Kori Wasu Kararraki da Aka Kalubalanci Nasarar Sanwo-Olu na Legas

Kotun Zabe Ta Kori Wasu Kararraki da Aka Kalubalanci Nasarar Sanwo-Olu na Legas

  • Kotun sauraron ƙarar zaben gwamna ta yanke hukunci kan nasarar gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas
  • Kwamitin alkalai uku karkashin mai shari'a Arum Ashom ta kori kararrain yan takarar LP da PDP, ta tabbatar da nasarar APC
  • A cewarsa Kotun, ta kori ƙarar ne saboda rashin cancanta domin ba ta da hurumin sauraron abin da ya shafi gabanin zaɓe

Jihar Lagos - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna ta yanke hukunci kan wasu ƙararraki da aka ƙalubalanci nasarar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Jaridar The Nation ta ce yayin zaman yanke hukunci ranar Litinin, Kotun ta kori ƙarar da Gbadebo Rhodes-Vivour da Labour Party suka shigar suna ƙalubalantar nasarar APC.

Kotu ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan Legas.
Kotun Zabe Ta Kori Wasu Kararraki da Aka Kalubalanci Nasarar Sanwo-Olu na Legas Hoto: Gbadebo Rhodes-Vivour, Olajide Adediran
Asali: Facebook

Haka nan kuma ta sake korar ƙarar Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor da jam'iyyarsa ta PDP, wanda suka shigar kan nasarar Sanwo-Olu a zaben da ya shuɗe.

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Legas

Jandor, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP ya nuna rashin gamsuwa da zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, inda ya ƙalubalanci nasarar gwamna Sanwo-Olu da Obafemi Hamzat a gaban Kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Sanwo-Olu

Vanguard ta ruwaito cewa Kotun ta tabbatar nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kwamitin alƙalai uku na Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen karkashin jagorancin mai shari'a Arum Ashom ya yi fatali da ƙarar saboda rashin cancanta.

Hukuncin wanda dukkan alƙalan suka aminta da shi, ya ce ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka gabatar, duk batutuwa ne da suka shafi gabanin zaɓe wanda Kotu ba ta da hurumi a kansu.

Sauran alƙalan da suka yanke wannan hukuncin sun ƙunshi, mai shari'a Mikail Abdullahi da kuma mai shari'a Igho Braimoh.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Gwamnonin Jam'iyyar PDP Da Suka Yi Nasara a Kotun Zabe

Sanwo-Olu ya samu kuri'u 762,134 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Rhodes-Vivour na LP wanda ya samu kuri'u 312,329. Dan takarar PDP, Adediran, ya zo na uku da kuri’u 62,449.

Kakakin Majalisar Osun Ya Tsallake Rijiya da Baya

A wani rahoton na daban Kakakin majalisar dokokin jihar Osun ya tsallake rijiya da baya yayin da haɗarin mota ya rutsa da ayarinsa a Osogbo.

Ayarin motocin kakakin majalisar ya gamu haɗarin ne yayin da suke shirin barin Osogbo, babban birnin jihar ranar 24 ga watan Satumba, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262