Jerin Sunayen Gwamnonin PDP Da Suka Yi Nasara a kotun Zabe
Kotunan sauraron ƙararrakin zaɓukan gwamnoni a Najeriya, na cigaba da zartar hukuncinsu kan ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarorin da wasu gwamnoni suka samu a zaɓen 2023.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yayin da wasu gwamnonin suka samu nasara a kotun, wasu kuma sun rasa kujerunsu bayan hukuncin kotun.
Legit.ng ta tattaro jerin sunayen gwamnonin da aka zaba a ƙarƙashin jam'iyyar PDP da suka yi nasara a kotun:
1. Bala Mohammed (Gwamnan Bauchi)
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kotun sauraren ƙararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a P.T Kwahar a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba ta tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed.
Kotun ta bayyana Gwamna Bala a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Bauchi na ranar 18 ga watan Maris.
Cikin Gwamnan APC Ya Kada, Kotu Ta Bayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Karar Da Ke Kalubalantar Nasararsa a Zabe
2. Peter Mbah (Gwamnan Enugu)
An tabbatar da Peter Mbah a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Enugu.
Kotun sauraren ƙararrakin zaben gwamnan jihar Enugu a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, ta yi watsi da dukkanin ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar gwamna Chijioke Edeogu na jam’iyyar Labour Party (LP) ya shigar yana kalubalantar nasarar Mbah a zaɓen.
3. Caleb Mutfwang (Gwamnan Plateau)
Kotun zaɓe ta kori ƙarar da ke kalubalantar nasarar Gwamna Caleb Mutfwang, wacce ɗan takarar jam'iyyar APC Nentawe Yilwatda, ya shigar.
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna da ke zamanta a Jos babban birnin jihar Plateau, a ranar Juma’a, 22 ga watan Satumba, ta tabbatar da nasarar gwamna Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP.
Mai shari’a Sunday Olorundahunsi, da ke karanta hukuncin a ranar Juma’a, ya yi watsi da dukkanin ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar jam'iyyar APC.
4. Dauda Lawal (Gwamnan Zamfara)
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Zamfara ta tabbatar da nasarar gwamna Dauda Lawal a zaɓen ranar Litinin, 18 ga watan Satumba.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna Bello Matawalle suka shigar inda suke ƙalubalantar ayyana gwamna Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Kotu Za Ta Yi Hukunci Kan Zaben Gwamnan Legas
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas ta shirya yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.
Kotun ta sanya ranar Litinin, 25 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta zartar da hukuncinta kan shari'ar da ke ƙaƙubalantar nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Legit.ng