Kotun Zabe Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Mutfwang Na Jihar Filato
- Kotun zaɓe mai zama a Jos ta tabbatar da nasarar gwamna Celeb Mutfwang na jam'iyyar PDP a zaben jihar Filato
- Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, Kotun ta ce ɗan takarar APC ba shi da hurumin kalubalantar harkokin da suka shafi PDP
- Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Kotun zabe ta tsige Abba Gida Gida daga kujerar gwamnan jihar Kano
Plateau - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna mai zama a Jos ta tabbatar da nasarar gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato a zaben 2023, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Mutfwang, ɗan takara a inuwar jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna ranar 18 ga watan Maris.
Amma Dakta Nentawe Yilwatda, ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, ya nuna bai yarda da sakamakon zaben ba, inda ya nufi Kotun zaɓe ya shigar da ƙara.
A ƙarar da ya shigar, ɗan takarar APC ya roƙi Kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe saboda jam'iyyar PDP ba ta da ingantaccen tsari kuma an yi aringizon ƙuri'u.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai ƙara ya kuma buƙaci Kotu ta shigar da ƙuri'un rumfunan zabe 14 da INEC ta soke, cikin sakamakon zaben da aka bayyana a baya.
Hukuncin da Kotu ta yanke kan haka
Da take yanke hukunci ranar Jumu'a, 22 ga watan Satumba, Kotun karkashin jagorancin mai shari'a R. Irele-Ifineh, ya ce ƙorafin rashin tsarin PDP batu ne da ya shafi gabanin zaɓe.
Alkalin ya ce korafin mai shigar da ƙara cewa jam'iyyar PDP ba ta da tsarin zama jam'iyya, abu ne da ya shafi harkokin kafin zaɓe kuma masu ƙara ba su da hurumin ƙalubalantar batun.
Kotun ta kuma yanke cewa ta gamsu cewa PDP ta sake gudanar da gangamin zaben shugabanninta ranar 25 ga watan Satumba, 2021 bisa umarnin babbar Kotun Jos.
Daga ƙarshe, Kotun ta kori ƙarar baki ɗaya bisa rashin cancanta, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
NNPP Ta Nada Sabon Mai Magana da Yawunta Na Kasa
A wani rahoton kuma Jam'iyyar NNPP ta naɗa sabon mai magana da yawunta na ƙasa jim kaɗan bayn martani kan hukuncin tsige Abba Gida-Gida.
NWC karkashin jagorancin Abba Kawu ya amince da naɗin Yakubu Shendam a matsayin sabon Sakataren yaɗa labarai na NNPP.
Asali: Legit.ng