Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Yi Nadamar Wasu Ayyuka da Ya Yi Lokacin Yana Mulki

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Yi Nadamar Wasu Ayyuka da Ya Yi Lokacin Yana Mulki

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ji ta dadi ba a lokacin da ya shugabanci kasar
  • Mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya yi nadamar abubuwa da dama a shekaru takwas da ya yi a mulki
  • A hirarsa da manema labarai, Adesina ya ki bayyana ainahin matsalolin da shugaban kasar ya fuskanta a lokacin da yake shugabanci amma ya ce ya yi danasani a mulkinsa

Osogbo, jihar Osun - Mista Femi Adesina, wanda ya yi aiki a matsayi mai ba da shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ubangidan nasa ya yi danasanin wasu abubuwa a gwamnatinsa.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Adesina ya yi magana ne a Osogbo a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, a wani taro da kungiyar shahararrun yan jarida suka shirya a jihar Osun.

Kara karanta wannan

“Ban Mutu Ba Lokacin Da Suka Binne Ni”: Lamarin Mohbad Ya Dauki Sabon Salo Inda Wani Ya Ga Mawakin a Mafarki

Femi Adesina ya ce Buhari ya yi nadamar wasu abubuwa a matsayin shugaban kasa
Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Yi Nadamar Wasu Ayyuka da Ya Yi Lokacin Yana Mulki Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Na yi wa Buhari tambayoyi masu tarin yawa kafin ya sauka daga mulki, Adesina

Kakakin tsohon shugaban kasar ya ce kafin Buhari ya bar mulki, ya yi hira da shi na tsawon awanni biyu, inda a nan ne ya yi masa duk wasu tambayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, a yayin hirar, ya tambayi ubangidan nasa menene danasaninsa, kuma Buhari ya nuna nadamar cewa da an yi wasu abubuwa ta wata hanya daban.

Koda dai Adesina bai bayyana danasanin Buhari ba ya ce:

"Babu wani dan adam a doron kasa da ba zai yi nadamar wasu abubuwa ba. Yana daya daga cikin tambayoyin da na yi wa shugaban kasar.
"Kafin mu bar mulki, na zauna da shi na kimanin awanni 2 sannan na tambaye shi duk wasu tambayoyi kuma a lokacin da muka kammala, ya tambayi me na ba babban mai tsara harkokinsa da ya ba da dogon lokaci haka don ganawa da shi. Babu tambayar da ban yi masa ba. Akwai abubuwan da shi (Buhari) yake ganin da an yi su fiye da yadda aka yi su."

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Fusata, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Matarsa Da Ta Roki Sarakuna a Madadinsa

Da yake ci gaba da magana, Adesina ya ce Buhari ya yi wa kasar hidima tukuru, amma ya kara da cewar duk inda aka lura da ba daidai ba a yadda ubangidansa ya shugabanci kasar, ba za a iya daura laifin a kansa shi kadai ba.

Kwankwaso Ya Maida Martani Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke a Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa an shawarci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya karbi hukuncin kotun zaben gwamna da kyakkyawar zuciya, sannan kada ya tunkari kotun daukaka kara ko na koli domin babu kwakkwarar hujja na soke hukuncin kotun zaben.

Tsohon kwamishinan raya karkara, Dr Ilyasu Musa Kwankwaso, ne ya yi wannan martanin jim kadan bayan kotun zaben ta ayyana Dr Gawuna Yusuf, na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zabe, rahoton Nigerian Tribune.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng