Kotun Amurka Ta Amince da Bukatar Atiku Kan Takardun Karatun Tinubu

Kotun Amurka Ta Amince da Bukatar Atiku Kan Takardun Karatun Tinubu

  • Kotun Majistire a ƙasar Amurka ta amince da buƙatar Atiku Abubakar na PDP kan takardun karatun Bola Tinubu a jami'ar jihar Chicago
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya roƙi Kotu ta bada umarnin tilasta wa jami'ar sakin dukkan takardun shugaba Tinubu
  • Sai dai Lauyoyin Tinubu sun faɗa wa Kotun cewa akwai takardun da wanda su ke karewa ba ya son a fitar da su

U. S - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu nasara kan karar da ya shigar a Kotun Amurka.

Channels tv ta rahoto cewa Kotun arewacin Illinois ta ƙasar Amurka ta amince da buƙatar da Atiku ya shigar gabanta ta sakin takardun karatun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Atiku da shugaba Tinubu.
Kotun Amurka Ta Amince da Bukatar Atiku Kan Takardun Karatun Tinubu Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku ya garzaya Kotun Amuraka ya roƙi ta umarci jami'ar jihar Chicago ta ba shi cikakkun takardun karatun shugaba Tinubu, wanda ya a can ya yi digirinsa na farko.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Jihar Arewa

Wane hukuncin Kotun Amurka ta yanke?

Da yake yanke hukunci ranar Talata, Alƙalin Kotun Majistire ta ƙasar Amurka, mai shari'a Jeffrey Gilbert, ya umarci jami'ar Chicago ta fidda, "Dukkan takardun kuma banda na sirri" ta bai wa Atiku cikin kwanaki biyu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan batu na gaban Kotu kan buƙatar Atiku Abubakar mai lamba 28 U.S.C. § 1782. Bisa dalilin da aka zayyano a ƙarar, Kotu ta amince da buƙatar," in ji Alkalin.

Lauyoyin Tinubu sun yi korafin cewa wanda suke karewa ba ya son ya cire alfarmar sirri na takardun karatunsa, inda hukuncin ya kuma amince da hakan ta hanyar amfani da kalmar "takardun da ba su alfarmar sirri."

Atiku dai ya garzaya kotu ne domin neman umurnin da zai tilastawa jami’ar Chicago sakin bayanan karatun shugaba Tinubu, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Maka Shugaban Kasa Tinubu a Gaban Kotu Kan Wani Muhimmin Abu 1

Duk da cewa takardun Tinubu sun nuna ya kammala karatun digirin farko a 1979 a fannin lissafin kudi, ana zargin akwai tufka da warwara a cikin takardun.

Abinda Ministan Kwadago Ya Fada Mana Kan Sabon Mafi Karancin Albashi, TUC

A wani rahoton na daban Ƙungiyar TUC ta bayyana abinda Ministan Kwadago ya faɗa mata game da ƙarin albashi ga ma'aikata.

Shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya ce Lalong ya ce musu ya zauna da shugaba Tinubu da Ministan kuɗi kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262