Malamin Addini Ya Gargadi Atiku da Obi, Ya Ce Guguwar Sauya Sheka Na Nan Tafe Ga LP da PDP
- Shugaban Cocin INRI, Primate Elijah Ayodele, ya ce ya hango gagarumar guguwar sauya sheƙa da ke shirin turnuƙe Labour Party
- Malamin cocin ya ƙara da bayanin cewa idan guguwar ta zo zata haɗa da babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP
- Saboda haka ya shawarci manyan jam'iyyun adawar guda biyu da su koma gida su sake shiri da dabaru kuma su tabbata sun yi abinda ya dace
FCT Abuja - Jagoran majami'ar INRI, Primate Elijah Ayodele, ya roƙi Peter Obi da Atiku Abubakar su hanzarta su, "Koma gida su gyara wurin da ya cukurkuɗe."
Mista Obi ne ya riƙe tutar takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP yayin da Atiku ya nemi zama shugaban ƙasa a babban zaben 2023 a inuwar jam'iyyar PDP.
Dukkanin 'yan takarar biyu suna fatan ɗare wa kujerar shugaban kasa saboda suna kalubalantar nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a gaban Kotu.
"Ina hango tulin sauya sheka a LP da PDP"
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter ranar Talata, 19 ga watan Satumba, 2023, Primate Ayodele ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ina son faɗa wa Atiku da Obi cewa akwai buƙatar su koma gida su gyara komai. Mutane da yawa zasu gudu su barsu daga watan Janairu, Fabrairu da Maris. Ina hango tulin sauya sheƙa a LP da PDP."
"Ya kamata PDP ta koma ta canza dabaru, ta yi abin da ya dace, ta gyara kana da biya buƙatun da ke ƙasa, kuna ganin mambobin majalisar can, to zasu sauya jam'iyya."
"Zaku gigice, kada ku yi mamaki akwai gwamnan da zai sauya jam'iyya ya barku. Ina faɗa muku abinda ke tunkaro ku ne kawai, kada ku yi mamakin hakan zai girgiza ku."
Kotun Zabe Ta Tsige 'Yan Majalisar Wakilai 25, Sanato 5 Daga Kan Kujerunsu
A wani rahoton kuma Tun bayan rantsar da majalisar tarayya ta 10, aƙalla 'yan majalisar wakilai 25 da Sanatoci 5 Kotu ta tsige daga kujerunsu.
Jam'iyyar APC ce ta fi kowace jam'iyya rasa Sanatoci yayin da kuma ita ce ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng