Atiku Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli Don Kalubalantar Nasarar Tinubu

Atiku Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli Don Kalubalantar Nasarar Tinubu

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya daukaka zuwa kotun koli kan zaben shugaban kasa
  • A farkon wannan watan ne kotun sauraran kararrakin zabe ta yi fatali da korafin Atiku kan rashin hujjoji
  • Kotun yayin yanke hukunci, ta tabbatar da Bola Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen shugaban kasa

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya daukaka kara zuwa kotun koli kan zaben shugaban kasa.

Atiku ya daukaka kara kan rashin nasarar da ya yi a farkon wannan wata inda kotu ta tabbatar da Bola Tinubu wanda ya lashe zabe, Legit ta tattaro.

Atiku ya daukaka kara kotun koli kan zaben Tinubu
Atiku Ya Sake Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli. Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe Atiku ya daukaka kara kan zaben Tinubu?

Abubakar ya bayyana haka ne a yau Talata 19 ga watan Satumba a birnin Tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

"Ba Zata Sabu Ba" Dan Majalisar Tarayya Na PDP Da Kotu Ta Tsige Ya Fusata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce hukuncin kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a, Haruna Tsammani akwai babban kuskure a ciki.

Babban lauyan Atiku, Chris Uche ya roki kotun koli da ta yi watsi da duk wasu matakai da kotun kararrakin zabe ta bi.

Meye Atiku ke nema kan zaben Tinubu?

Da su ke daukaka kara a kotun koli, wakilan Atiku sun zargi hukuncin Haruna Tsammani da tawagarsa da kin gaskiya karara da kuma tauye hakkin mai kara.

Har ila yau, Atiku ya zargi kotu da kin bin diddigin matsalolin da aka samu na sabawa dokokin zabe yayin da gudanar da shi.

Wannan na zuwa ne bayan kotun ta sallami dan takarar PDP, Atiku Abubakar da kuma takwaransa na jam'iyyar Labour, Peter Obi.

'Yan takarar jam'iyyun guda biyu tun farko sun kalubalanci zaben da su ka ce na cike da magudi da saba dokokin zabe.

Kara karanta wannan

MURIC Ta Yi Gargadi Ga Gamayyar Fastoci, Ta Ce Barazanarsu Ba Abin Da Zai Yi Ga Alkalan Kotun Koli

'Asarar kudinku za ku yi', Fasto ya gargadi Atiku, Obi

A wani labarin, Shahararren Fasto mai suna Elijah Ayodele ya yi martani kan hukuncin zaben da ake a kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa.

Elijah ya ce da 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyun PDP da Labour, kawai asarar kudinsu za su yi a kotun koli.

Ya ce Peter Obi da Atiku Abubakar kada su bata lokacinsu wurin zuwa kotun koli don ba za su samu nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.