Kano: Kotun Zabe Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Nasarar Abba Gida-Gida
- Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta sanar da ranar yanke hukunci kan nasarar Abba Gida-Gida
- Tawagar lauyoyin NNPP mai kayan marmari ta tabbatar da cewa kotu ta sanya ranar Laraba a matsayin ranar yanke hukunci
- Jam'iyar APC ce ta shigar da ƙara mai ƙalubalantar nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida
Jihar Kano - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar Kano ta sanya ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, 2023 domin yanke hukunci kan sahihancin nasarar NNPP.
Daily Trust ta tattaro cewa jam'iyyar APC ce ta shigar ƙara ta kalubalanci nasarar Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.
Kotun zaɓen ta sanar da ranar yanke hukuncin ne a wata takardar sanarwa da ta aike wa kowane ɓangare ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023.
NNPP na fatan Kotu ta kori ƙarar
Sakataren tawagar lauyoyin NNPP, Barista Bashir T/Wurzici, wanda ya tabbatar da batun sanya ranar hukunci, ya ce an mika musu sanarwar da yammacin ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi farin ciki saboda a yanzu ranar hukunci ta zo hannu, haka nan kuma muna cikin farin ciki domin mun san kotu zata kori ƙarar ne kawai kuma ta ci su tara."
"Muna fatan kotun za ta bi matakin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta bi wajen yanke hukunci saboda al'amuran iri daya ne," in ji shi.
Muna sa ran samun nasara - APC
A nasa bangaren, mataimakin shugaban APC a Kano, Shehu Maigari, ya ce suna sa ran hukuncin “Zai mana daɗi bisa ga hujjojin da muka mika wa kotun, muna kyautata zaton za mu yi nasara."
“Ba mu tsoron komai saboda muna da kwarin gwiwa a kan takardun shaidun da muka gabatar. Don haka muna da kyakkyawan fata bisa ga abin da muka gabatar.”
Hasashen hukuncin da Kotu zata yanke ya haifar da tashin hankali a jihar inda bangarorin biyu suka riƙa shirya addu'o'in neman taimakon Allah, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Gwamnatin Tinubu da NLC Ba Su Cimma Matsaya Ba, Za Su Sake Gana Wa Yau
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya da ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC sun tashi taro baram-baram ba a cimma komai ba.
Rahoto ya nuna ministan kwadago, Simon Lalong, ya sake shirya gana wa da wakilan ƙungiyar 'yan kasuwa TUC.
Asali: Legit.ng