Ondo: Kakakin Majalisa Ya Musanta Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna
- Majalisar dokokin jihar Ondo ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa tana shirin tsige mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa
- Kakakin majalisar, Olamide Oladiji, ya ce labarin ba gaskiya bane kuma ba bu wani shiri da majalisa take yi a ƙarƙashin kasa
- Shugaban masu rinjaye ya jaddada kalaman kakakin majalisar, ya ce sun maida hankali wajen ci gaban jihar Ondo
Jihar Ondo - Majalisar dokokin jihar Ondo ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa tana shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Honorabul Lucky Aiyedatiwa.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an yi ta cece-kuce da yaɗa jita-jita a ciki da wajen jihar cewa nan ba da jimawa ba majalisar za ta fara aikin tsige shi daga kujerar mataimakin gwamna.
Kwanaki kaɗan bayan dawowa daga hutun jinya, gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo ya kori dukkan hadiman midiya da ke ofishin mataimakin gwamnan bisa zargin rashin biyayya.
Akeredolu, ya kuma umarci ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a da ta kula da harkokin midiya na ofishin mataimakin gwamna, Premium Times ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene gaskiya kan shrin tsige mataimakin gwamna?
Da yake magana kan shirin tsige mataimakin gwamnan, kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Honorabul Olamide Oladiji, ya ce:
"Babu wani shiri da muke ta ƙarƙashin ƙasa na tsige mataimakin gwamna, ba bu wani abu makamancin haka, kun san kafafen sada zumunta za su iya rubuta son ransu amma ba gaskiya bane."
"Babu wani abu mai kama da shirin tsige mataimakin gwamna.Yanzu da muke magana ina Abuja zan halarci taron shugabannin majalisun jihohi, saboda haka rahoton kanzon kurege ne."
Da yake jaddada kalaman kakakin majalisa, shugaban masu rinjaye na majalisar Ondo, Oluwole Ogunmolasuyi, ya roƙi jama'a su yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa.
"Mun shagaltu da abin da zai kawo ci gaba a jihar. Abin da ke da muhimmanci a gare mu shi ne gudanar da ayyukanmu."
Shugaban Matasa da Hadiman Gwamnan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Bayelsa
A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Bayelsa na jam'iyyar PDP ya ƙara rasa manyan makusanta yayin da ake tunkarar zaben gwamna a watan Nuwamba.
Masu baiwa gwamna Diri shawara ta musamnan 3 da shugaban matasan PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng