Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Zabe
- Gwamna Dauda Lawal ya nuna jin daɗinsa dangane da hukuncin da Kotu ta yanke kan zaben gwamnan jihar Zamfara
- Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta tabbatar da nasarar Lawal na jam'iyyar PDP bayan ta ƙori karar Bello Matawalle na APC
- Da yake martani kan hukuncin, gwamnan ya ce hakan ya tabbatar da zaɓin da mutane suka yi a watan Maris
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben gwamana ta yanke a matsayin tabbatar da muraɗin Zamfarawa.
Lawal, ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaɓen jihar Zamfara a watan Maris, 2023, inda ya kayar da gwamna mai ci, Bello Matawalle, Punch ta ruwaito.
A ɗazu ne Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben gwamnan Zamfara mai zama a Sakkwato ta tabbatar da nasarar Lawal a matsayin sahihin gwamnan jihar da ke Arewa maso Yamma.
Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Gwangwaje Mai A-Daidaita-Sahun Da Ya Mayar Da N15m, Da Muhimmin Abu 1
Gwamna Lawal ya maida martani kan nasarar da ya samu a Kotu
Gwamna Lawal ya jaddada cewa hukuncin da Kotun zaɓen da yanke ya yi dai-dai da zaɓin mutanen jihar Zamfara, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi wannan furucin ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Idris, ya fitar ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, 2023 a Gusau.
Sanarwan ta ce:
"Sa'o'i kaɗan da suka wuce aka tabbatar da Lawal a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen gwamnan jihar Zamfara ranar 18 ga watan Maris, 2023 a Kotun zaɓe mai zama a jihar Sakkwato."
"Ba abun mamaki bane don Kotu ta yanke wannan hukuncin sai dai ta tabbatar da muradi da zaɓin ɗaukacin mutanen jihar Zamfara."
Idan baku manta ba, Lawal na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 377,726, inda ya lallasa tsohon gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Bello Matawalle, wanda ya samu ƙuri'u 311,976.
Da Dumi-Dumi: Kotun Sauraran Korafe-korafen Zabe Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Da Ake Na Gwamnan jihar Arewa
Gwamna Sanwo-Olu Ya Sauya Wa Wasu Hadimansa Wurin Aiki a Jihar Legas
A wani labarin kuma Mista Babajide Sanwo-Olu ya canza wa wasu daga cikin masu ba shi shawara ta musamman ma'aikatun da za su yi aiki.
Gwamnan Sanwo-Olu na Legas ya sanar da sauye-sauyen ne a wurin taron maraba da aka shirya wa sabbin mambobim majalisar zartarwa.
Asali: Legit.ng