APC Na Shirin Dakatar da Shugaban Jam'iyya a Jihar Ondo
- Jam'iyyar APC ta fara shirin ɗaukar tsattsauran mataki kan shugabanta wanda ya sa hannu aka lakaɗa wa kwamishinar mata duka
- Shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya ce ba zasu lamurci rin wannan rashin ɗa'a da ladabi a jam'iyyar ba
- A ranar Lahadi, wasu mutane suka zane kwamishinar mata yayin rabon kayan tallafi a karamar hukumar Akoko
Jihar Ondo - Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo ta ayyana cewa zata hukunta shugaban jam'iyyar na gunduma guda a ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma, Mista Olumide Awolumate.
Jaridar Punch ta tattaro cewa APC na shirin ladabtar da shi ne biza zarginsa da hannu a bugun kwamishinar harkokin mata ta jihar Ondo, Misis Juliana Osadahun.
Wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a soshiyal midiya ya nuna shugaban jam'iyyar ya shiga cikin bara gurbi suka laƙaɗa wa kwamishinar duka, ana zargin har rauni suka ji mata.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne lokacin da kwamishinar ta je rabon kayan tallafin rage raɗaɗi a garin Arigidi Akoko ranar Lahadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba zamu bar abun ya wuce haka nan ba - APC
Da yake zantawa da 'yan jarida ranar Litinin, shugaban APC na jiha, Mista Ade Adetimehin, ya nuna takaicinsa game da farmakin da aka kai wa kwamishinar.
Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC za ta kira zama na musamman kan lamarin yau (watau ranar Litinin, 18 ga watan Satumba), kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.
A kalamansa ya ce:
“Ba mu yarda da rashin da’a a jam’iyyarmu ba. Za a dakatar da shugaban jam'iyya saboda kuskuren da ya tafka na shiga cikin irin wannan aikin, abin kunya."
“Na umarci shugaban APC na karamar hukumar ya kirawo kowa zuwa Akure a yau (Litinin) kuma za mu ɗauki matakin da ya dace a inda ya dace. Amma za a dakatar da shugaban gundumar.”
Tashin Hankali: Matashi Ya Lakadawa Kwamishinar Mata Tsinannen Duka Kan Rabon Kayan Tallafi, An Bayyana Dalili
Gwamnan Jihar Filato Ya Nada Sabbin Hadimai 136 a Gwamnatinsa
A wani rahoton na daban Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya amince da naɗa sabbin hadimai 136 a matsayin mambobin majalisar zartarwa.
Sai dai gwamnan bai bayyana muƙaman da ya naɗa sabbin mataimakan ba har kawo yanzu amma sanarwan ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da su aikin da zasu yi.
Asali: Legit.ng