Kotun Zabe: Cikakken Sunayen Yan Majalisar Wakilai Na Labour Party Da Za Su Sake Takarar Zabe
Kotun sauraron kararrakin zaben majalisun dokokin tarayya ta tsige wasu mambobin majalisar wakilai sannan ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta gudanar da sabon zabe a mazabun da abun ya shafa.
Babbar jam'iyyar adawa ta biyu a Najeriya, Labour Party, wacce ta yi nasarar samun wasu yan kujeru a majalisar wakilai da majalisar dattawa, ta hadu da gagarumin cikas yayin da kotun zaben ta tsige wasu mambobinta sannan ta soke nasarar da suka yi a zaben.
A wannan rahoto Legit Hausa ta jero mambobin majalisar wakilai na jam'iyyar LP da suk sake takara a sabon zaben da INEC za ta yi a wakonni da watanni masu zuwa.
1. Mista Ibe Okwara Osunwa (Jihar Abia)
Zababben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Arochukwu/Ohafia ta jihar Abia, Ibe Okwara Osonwa, yana cikin wadanda kotun zabe ta soke nasararsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun zaben yan majalisun tarayya da ke zama a Umuahia, babban birnin jihar Abia ta tsige Osonwa, dan majalisar da aka zaba karkashin inuwar Labour Party a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba.
Zai gwabza da dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daniel Okeke, a zaben da za a sake yi.
2. Munachim Alozie (Jihar Abia)
Wani kwamiti karkashin jagorancin Mai shari'a Hajaratu Hajjo Lawa ya soke zaben Munachim Alozie, dan majalisa mai wakiltar mazabar Obingwa/Osisioma/Ugwunagbo a jihar Abia.
Dan majalisar tarayyar zai yi takara a sabon zaben da INEC za ta gudanar.
A halin da ake ciki, za a gudanar da zaben da INEC ta yi umurni ne cikin kwanaki 90 masu zuwa kamar yadda yake a kundin tsari.
Alozie zai fafata a zaben da dan takarar Young Progressives Party, Ibe Michael Nwoke.
3. Mista Emeka Nnamani (Aba ta arewa da kudu)
Hakazalika, kotun zaben jihar Abia ta soke zaben mamba mai wakiltar maabar Aba ta arewa da kudu, Mista Emeka Nnamani, kan gabatar da satifike na bogi.
Kotun zaben ta ayyana dan takarar All Progressives Grand Alliance a zaben Alex Ikwueche a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ya umurci INEC da ta janye takardar shaidar cin zaben da ta bai wa Nnamani da bai wa Ikwueche sabo.
4. Thaddeus Atta (Eti-Osa, jihar Lagos)
Kotun zabe a jihar Lagas ta tsige tare da soke nasarar Honourable Atta Achief Thaddeus, zababben dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Eti-Osa.
Atta zai fafata da Bankole ‘Banky W’ Wellington, da Olajide Obanikoro a zaben.
5. Farfesa Sunday Nnamchi (Enugu ta gabas)
Kotun zabe a jihar Enugu ta soke nasarar dan majalisa mai wakiltar mazabar Enugu East/Isi-Uzo ta jihar Enugu.
Dan majalisar da aka tsige, Farfesa Nnamchi ya umurci tawagar lauyoyinsa da su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.
Zai yi takara a sabon zaben da hukumar INEC za ta gudanar.
Mataimakin gwamnan jihar Ondo ya musanta raɗe-radin murabus daga Mukaminsa
A wani labarin kuma, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Mista Lucky Aiyedatiwa, a ranar Juma’a, ya musanta rattaba hannu kan wata takarda ta ajiye aiki kamar yadda ake yayatawa a wasu bangarori.
Mista Aiyedatiwa ya ce bai san komai ba game da takardar murabus ɗin da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta a baya bayan nan, kamar yadda Punch ta rahoto.
Asali: Legit.ng