Jami'ar Jihar Chicago Ta Saki Takardun Shaidar Karatun Shugaba Tinubu
- Jami'ar jihar Chicago (CSU) ta saki kwafin takardun shaidar karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Kwafin takardun wanda hadimin shugaban ƙasan ya sanya a ranar 15 ga watan Satumba, an sake shi ne yayin da ake cigaba da ƙarar da Atiku ya shigar domin samun bayanan takardun karatun Tinubu
- A baya jami'ar ta bayyana cewa ba za ta iya ba da shaidar difloma ta Tinubu a bisa rantsuwa ba, amma ta tabbatar ya halarci makarantar tare da kammala karatunsa
Daga ƙarshe jami'ar jiha Chicago ta saki kwafin takardun karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Hadimin shugaban ƙasan kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun shi ne ya sanya kwafin takardun karatun a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba.
Legit.ng ta lura da cewa an saki kwafin takardun karatun ne bayan Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, ya shigar da ƙara a wata kotun Amurka domin tilasta jami'ar ta ba shi takardun karatun Shugaba Tinubu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ƴan Najeriya sun yi martani kan takardun karatun Tinubu
Odekina Alilu ya rubuta a Facebook cewa:
"Dukkanin ƴan siyasa yakamata su ƙyale shugaban ƙasa ya mayar da hankali kan matsalolin da ke fuskantar ƙasarmu Najeriya.
"Mu manta da batun takardar shaidar Chicago. Abin da muka fi so daga wajensa shi ne ƙoƙarinsa na fitar da ƙasar nan daga ƙangin da shugabannin da suka shuɗe suka jefata, mu mara masa baya da addu’o’in samun nasara domin wannan ƙasa tamu Najeriya.”
AY Deeni ya rubuta:
"Alhaji Atiku Abubakar, mun gode domin neman samun takardun shaidar karatun Tinubu. Yanzu muna buƙatar na ka da na Gbajue."
Bola Tinubu, Ganduje da Manyan Hafsoshin Tsaro Sun Yi Kus-Kus Kan Abu 1 a Villa, Ƙarin Bayani Ya Fito
Idike K Chris ya yi tambaya:
"Takardun shaidar karatun wa? Namiji ko macen Tinubu?"
Tinubu Baya Son Kotu Ta Ba Atiku Takardun Karatunsa
A baya rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa kotu bayanin dalilan da ya sanya baya son jami'ar jihar Chicago ta ba Atiku Abubakar, takardun karatunsa.
Hakan na zuwa ne dai bayan Atiku Abubakar ya shigar da ƙara a Amurka, yana neman kotu ta tilasta jami'ar ba shi bayanan karatun Tinubu.
Asali: Legit.ng