Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna Fubara da Wasu Masu Ruwa da Tsaki a Ribas

Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna Fubara da Wasu Masu Ruwa da Tsaki a Ribas

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar Ribas karkashin jagorancin gwamna Siminalayi Fubara
  • Tawagar masu ruwa da tsakin sun je fadar shugaban kasa ne domin gode wa Tinubu bisa naɗa 'ya'yansu maza da mata a gwamnatinsa
  • Daga cikin waɗanda shugaban ƙasa ya naɗa daga jihar Ribas harda Nyesom Wike, wanda ya halarci taron yau Alhamis

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, da wasu masu ruwa da tsakin jihar mai arziƙin man fetur.

Wannan gana wa, wacce ta gudana a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, ta samu halartar Nyesom Wike, ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Gwamna Fubara da Wasu Masu Ruwa da Tsaki a Ribas Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Channels tv ta rahoto cewa gwamna Fubara na jam'iyyar PDP ne ya jagoranci tawagar masu ruwa da tsakin jiharsa zuwa wurin shugaba Tinubu yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Tarayya Ya Samu Babban Saɓani da Gwamnan APC Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Me suka tattauna da Tinubu a taron?

Da yake hira da 'yan jarida jim kaɗan bayan fitowa daga taron wanda ya gudana cikin sirri, tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), Onueze Okocha, ya yi magana kan gyara titin Gabas-Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okocha (SAN) ya bayyana cewa titin yana da matuƙar muhimmanci ga matatan man Patakwal, wacce gwamnatin shugaba Tinubu ta lashi takobin farfaɗo da ita, ta ci gaba da tace mai.

Ya ce masu ruwa da tsaki sun je Villa ne domin yaba wa shugaba Tinubu bisa naɗa ‘ya’yan jihar Ribas maza da mata a majalisar ministocinsa da sauran mukamai.

Daga cikin waɗanda Bola Tinubu ya naɗa har da Wike da kuma mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale.

A cewar Okocha, al’ummar jihar Ribas sun yi farin ciki da naɗe-naɗen da aka yi musu, kuma suna da kwarin gwiwar cewa wadanda aka nada za su sanya jihar alfahari.

Kara karanta wannan

Hadimai 2 Na Gwamnan PDP da Wasu Manyan Jiga-Jigai Sun Koma APC Ana Dab Da Sabon Zaɓe

Ya kara da cewa matakin da shugaba Tinubu ya dauka ya nuna cewa yana wakiltar muradun daukacin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da siyasa ko wata alakarsu ba.

Majalisar Kansiloli Ta Tsige Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Ogun

A wani rahoton kun ji cewa Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun, Honorabul Wale Adedayo daga kan muƙaminsa.

Wannan mataki ya biyo bayan dakatarwan da aka masa bisa zargin karkatar da kuɗaɗen al'ummar ƙaramar hukumar da yake shugabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262