Majalisar Kansiloli Ta Tsige Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Ogun
- Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun, Honorabul Wale Adedayo daga kan muƙaminsa
- Wannan mataki ya biyo bayan dakatarwan da aka masa bisa zargin karkatar da kuɗaɗen al'ummar ƙaramar hukumar da yake shugabanta
- Ciyaman din ya bayyana a gaban Kansilolin yau Alhamis kuma ya amince da duka tuhume-tuhumen da ake masa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Kansilolin ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun sun tsige shugaban ƙaramar hukumar, Honorabun Wale Adedayo daga kan kujerarsa kan wasu tuhume-tuhume.
A rahoton Punch, majalisar kansilolin sun sauke Ciyaman din daga muƙaminsa ne kan zargin wawure kudi da karkatar da kudaɗen asusun ƙaramar hukumar da sauran zargin da ake masa.
Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da shugaban majalisar kansilolin Ijebu ta gabas, Honorabul Fasheyi Akindele, ya fitar yau Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2023.
Ya ce tun farko sun dakatar da shugaban ƙaramar hukumar ne bayan ya tabbatar da alaƙa da tuhume-tuhumen da ake masa, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwan ta ce:
"Kansilolin karamar hukumar Ijebu ta gabas, Ogun sun tsige shugaban karamar hukumar da aka dakatar, Wale Adedayo, bisa zargin karkatar da kudade da wawure kudaden al'umma, da dai sauran zarge-zargen da ake yi masa."
"Bayan gayyatar da majalisar ta masa ya ƙi zuwa, Adedayo ya bayyana a gaban majalisar kansilolin a yau yayin da suka ci gaba da bincikarsa. Da bakinsa a gaban Kansiloli 11 ya amince da karkatar da kuɗaɗen yankin."
"Saboda haka shugaban majalisar kansilolin ya ayyana tsige Mista Wale Adedayo daga matsayin shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas.”
A safiyar yau ne Adedayo ya gurfana gaban ‘yan majalisar dokokin karamar hukumar domin kare zargin almubazzaranci da almundahana da ake yi masa.
Wakilin Punch ya tattaro cewa Adedayo ya isa sakatariya tare da wasu hadimansa guda biyu da misalin karfe 7:47 na safe, kuma sai ƙarfe 10:22 kansilolin suka kira shi, ya fito da misalin karfe 12:02 na rana.
Kotun Zabe Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna Sule a Jihar Nasarawa
A wani labarin kuma Kotun zaɓe mai zama a Lafia, babban birnin Nasarawa ta tanadi hukunci kan sahihincin nasarar gwamna Sule a zaben 2023.
Ɗan takarar jam'iyyar PDP ya shaida wa Kotu cewa shi ya samu ƙuri'u mafi rinjaye amma INEC ta bayyana sakamako na daban.
Asali: Legit.ng