Kotun Daukaka Kara Ta Janye Hukuncin Kotun Da Ta Bai Wa Elumelu Nasarar Lashe Zabe

Kotun Daukaka Kara Ta Janye Hukuncin Kotun Da Ta Bai Wa Elumelu Nasarar Lashe Zabe

  • Kotun daukaka kara a Abuja ta mayar da Ngozi Okelie kujerarshi a matsayin zababben dan majalisar dokoki
  • Kotun ta rusa hukuncin kotun jihar da ta bai wa Ndudi Elumelu nasarar a ranar 24 ga watan Yuli
  • Ngozi Okelie wanda dan Jam'iyyar Labour ne ya rasa kujerarshi bayan kotun zabe a jihar Delta ta rusa nasarar zabenshi

Jihar Delta - Kotun daukaka kara a Abuja ta rusa nasarar Ndudi Elumelu na jam'iyyar PDP.

Elumelu shi ne dan majalisar Tarayya da ke wakiltar Aniocha/Oshimili da ke jihar Delta, Legit ta tattaro.

Kotun daukaka kara ta rusa hukuncin kotu na nasarar Elumelu a jihar Delta
Ndudi Elumelu ya rasa damarshi ta kasancewa dan majalisar dokoki. Hoto: Honndudielumelu.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yi kan zaben Elumelu?

Kotun ta rusa hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe a jihar da ta ba shi nasara a ranar 24 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abin Mamaki Yayin Da Aka Dauke Wutar Lantarki Gaba Daya A Najeriya, An Fadi Dalili

A yayin hukuncin kotun a yau, ta tabbatar da Ngozi Okolle na jamiyyar Labour a matsayin wanda ya lashe zaben, cewar The Nation.

Kotun ta soki hukuncin da ya bai wa Elumelu nasara da cewa ya saba doka na rusa zaben Okolle a matsayin sahihin wanda ya lashe zabe.

Wace matsaya kotun ta bayar na zaben Elumelu?

Kotun ta amince ce da lauyan jamiyyar Labour, Mahmud Magaji (SAN) na cewa Okolie an zabe shi kuma jam'iyyar ce ta dauki nauyinshi.

Alkalan kotun su ka ce Okolie ya ajiye aikinshi na hadimin gwamnatin jihar Delta kamar yadda doka ta tanadar.

Wannan na zuwa ne bayan kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Delta ta bai wa Ndudi Elumelu nasarar zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Ngozi Okelie na jam'iyyar Labour ya daukaka kara zuwa kotu a Abuja inda a yanzu ta mayar masa da kujerarshi ta dan majalisar dokoki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Labour Party, Ta Bai INEC Sabon Umurni

Kotun Ta Kwace Kujerar Dan Majalisa Na NNPP, Ta Bai Wa APC a Kano

A wani labarin, kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya ta tsige Idris Dankawu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) daga kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kumbotso ta jihar Kano.

Channels Tv ta rahoto cewa kotun ta tsige Dankawu kan kirkirar takardar jarrabawarsa ta WAEC wacce ya gabatar domin shiga zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.