Gwamna Sanwo-Olu Na Lagos Ya Rantsar da Kwamishinoni 37 da Hadimai
- Daga ƙarshe, kwamishinoni 37 da masu bai wa gwamna shawara ta musamnan sun karbi rantsuwar kama aiki a jihar Legas
- An sha taƙaddama kan jerin sunayen kwamishinonin tsakanin gwamna Babajide Sanwo-Olu da majalisar dokokin jihar
- Majalisar da riƙa watsi da wasu mutanen kuma ta amince da wasu, na karshe ya samu shiga ne awanni 24 kafin bikin rantsuwa
Jihar Lagos - Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, a ranar Laraba, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 38 da masu ba da shawara na musamman, Daily Trust ta rahoto.
Jaridar Punch ta tattaro cewa bikin rantsuwar kama aikin ya gudana ne a ɗakin taron Adeyemi Bero Auditorium da ke Alusa a Ikeja, babban birnin jihar Legas.
Bayan kwan-gaba kwan-baya, majalisar dokokin jihar ta amince da sunayen mutum 38 da gwamnan zai naɗa a matsayin mambobin majalisar kwamishinoni.
Na ƙarshe da majalisar ta aminta da naɗinsa shi ne, Mista Tolani Akibu, wanda ta tabbatar da shi awanni 24 gabanin bikin rantsuwar kama aiki, kamar Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen mutanen da gwamna Sanwo-Olu ya rantsar
Waɗanda gwamnan ya bai wa rantsuwar kama aiki yau sun haɗa da, Layode Ibrahim, Mista Mobolaji Ogunlende, Dakta Dolapo Fasawe, Bola Olumegbon, Mista Idris Aregbe, Mis Abisola Olusanya, da Mista Moruf Fatai.
Sauran sun ƙunshi, Mista Kayode Bolaji-Roberts, Abiola Olowu, Misis Toke Benson-Awoyinka, Dakata Oreoluwa Finnih-Awokoya, Mista Yakub Alebiosu, Mista Lawal Pedro SAN, da Mr Tunbosun Alake.
Sai kuma Mista Gbenga Oyerinde, Dakta Adekunle Olayinka, Dakta Jide Babatunde, Mista Afolabi Ayantayo, Mista Tokunbo Wahab, Mista Olakunle Rotimi-Akodu, Jamiu Alli-Balogun, da Abdulkabir Ogungbo,
Haka zalika Dakta Afolabi Tajudeen, Mista Oluwaseun Osiyemi, Farfesa Akin Abayomi, Dakta Oluwarotimi Fashola, Misis Folashade Ambrose-Medem, da Misis Akinyemi Ajigbotafe duk suna cikin waɗanda suka rantse.
Ragowar mutanen su ne, Misis Bolaji Dada, Misis Barakat Bakare, Olugbenga Omotoso, Mosopefoluwa George, Dakta Yekini Agbaje, Dakta. Olumide Oluyinka, Abayomi Oluyomi, Dakta Iyabode Ayoola, Sola Giwa, da kuma Tolani Akibu.
Majalisar Dokokin Ogun Ta Karbi Sunayen Kwamishinoni 10 da Gwamna Ya Nada
A wani labarin kuma Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tura ƙarin sunayen mutum 10 da ya naɗa kwamishinoni zuwa majalisar dokoki.
Majalisar ta tabbatar da zuwan sunayen, kuma ta fara shirye-shiryen fara tantance su ranar Laraba, 13 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng