Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP Na Enugu Ta Yamma

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP Na Enugu Ta Yamma

  • Sanatan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai wakiƙtar Enugu ta Yamma a majalisar dattawa, Osita Ngwu. ya yi nasara a kotun zaɓe
  • Kotun sauraron ƙararrakin ƴan majalisun tarayya ta yi fatali da ƙararrakin da abokan takararsa na jam'iyyun APC da Labour Party suka shigar
  • Kotun ta yi fatali da ƙararrakin ne da ke ƙalubalantar nasarar Ngwu saboda rashin ingancin da su ke da shi

Jihar Enugu - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya mai zamanta a jihar Enugu, ta tabbatar da nasarar Injiniya Osita Ngwu, sanatan da ke wakiltar Enugu ta Yamma, cewar rahoton Leadership.

Bayan hukumar zaɓe ta bayyana Osita ɗan takarar jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, abokan takararsa na jam'iyyar Labour Party, Dennis Oguerinwa Amadi da Nicholas Eze na jam'iyyar APC sun shigar da ƙara a kotu.

Kara karanta wannan

Gaya vs Sumaila: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Sanatan Kano Ta Kudu

Kotu ta tabbatar da nasarar Sanata Ngwu
Kotu ta tabbatar da nasarar Sanata Osita Ngwu na PDP Hoto: Engineer Osita Ngwu RG
Asali: Facebook

Kotu ta zartar da hukunci

Kotun wacce mai shari'a A.M. Abubakar yake jagoranta, ta yi hukunci cewa ƙarar da Amadi ya shigar, ya tafka babban kuskure.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta bayyana cewa ɗan takatar na Labour Party ya yi kuskuren ne ta hanyar haɗa zarge-zargen rashin gudanar da zaɓen bisa tanadin sabuwar dokar zaɓe da zargin cin hanci da rashawa.

Kotun ta kuma bayyana cewa kamata ya yi yai shigar da ƙararrakin daban-daban sannan ya kawo hujjojin da za su kare ƙarar da ya shigar.

A hukuncin da kotun ta yanke, ta yi fatali da ƙarar Dennis Amadi bisa rashin ingancinta.

Hakazalika, Sanata Ngwu ya yi nasara akan Nicholas Eze na jam'iyyar APC a kotun zaɓen, rahoton Premium Times ya tabbatar.

A hukuncin da kotun ta yanke, ta yi fataƙi ɗa ƙarar ɗan takarar na jam'iyyar APC saboda rashin inganci.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Zaben 'Yar Majalisar PDP a Jihar Arewa, Ta Ba Dan Takarar APC Nasara

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Kawu Sumaila

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya mai zamanta a birnin Ƙano, ta tabbatar da nasarar Abdulrahman Kawu Sumaila n jam'iyyar NNPP a matsayin sanatan Kano ta Kudu.

Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da Kabiru Gaya na jam'iyyar APC ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Kawu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel