Kotu Ta Soke Zaben Beni Lar Yar Majalisar PDP a Jihar Plateau
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya a Plateau ta sake soke zaɓen ƴar majalisar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)
- Kotun ta soke zaɓen Beni Lar ƴar majalisa mai wakiltar mazaɓar Langtang ta Arewa/Langtang ta Kudu a majalisar wakilai
- Haka kuma kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Vincent Bulus a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Plateau - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya a jihar Plateau, ta soke nasarar ƴar takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Beni Lar, a mazaɓar Langtang ta Arewa/Langtang ta Kudu.
Lar, wacce wannan ne karonta na biyar tana zuwa majalisar wakilai, an zaɓe ta ne domin wakiltar mazaɓar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Jaridar The Punch ta ce mai shari'a Muhammad Tukur, wanda ya jagoranci yanke hukuncin kotun ranar Talata, 12 ga watan Satumba, ya ɗora alhakin soke zaɓen Lar bisa gazawar jam'iyyarta na gudanar da zaɓen fidda gwani domin tsayar da ita takara.
Don haka sai kotun ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, Vincent Bulus, a matsayin halastaccen wanda ya lashe, rahoton The Nation ya tabbatar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lar ta zama ƴar majalisa ta huɗu daga cikin ƴan majalisun PDP ta kotun zaɓen ta soke nasararsu a jihar.
PDP ta yi martani
A halin da ake ciki, jam'iyyar PDP ta nuna takaicinta kan yadda kotun zaɓen ta soke zaɓen ƴan takararta a jihar.
Da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Jos a ranar Talata, shugaban jam'iyyar na jihar, Chris Hassan, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin wanda ya ci karo da zaɓin jama'a waɗanda suka fito suka zaɓi ƴan takararta a lokacin zaɓen 2023.
Fashola Ya Magantu Kan Rashin Mukami
A wani labarin kuma, tsohon ministan gidaje da ayyuka, Babatunde Raji Fashola, ya yi magana kan rashin samun muƙami da ya yi a gwamnatin Tinubu.
Fashola ya bayyana cewa zai cigaba da taka rawarsa a matsayin ɗan ƙasa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya yi nuni da cewa ba kowa ba ne dama zai samu muƙami a gwamnati.
Asali: Legit.ng