Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Gwale

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Gwale

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Ciyaman ɗin karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso, bisa zargin sayar da kadarorin gwamnati
  • Shugaban majalisa, Yusuf Isma'il Falgore, ya ce wasu daga cikin Kansilolin yankin ne suka shigar da ƙorafi kan Ciyaman
  • A halin yanzu majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da bincike kana ta umarci mataimakin ciyaman ya maye gurbin na tsawon wata 3

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Honorabul Khalid Ishaq Diso, na tsawon watanni uku.

Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne yayin da ta amince da rahoton kwamitin kula da harkokin kananan hukumomi da naɗe-naɗen sarauta a zamanta na ranar Talata.

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da ciyaman na Gwale.
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Gwale Hoto: Punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa majalisar ta yi haka ne bayan an kawo mata ƙorafin cewa shugaban ƙaramar hukumar na sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da LP, Kotun Zaɓen NASS Ta Yanke Hukunci

A cewar majalisar, shida daga cikin Kansilolin ƙaramar hukumar Gwale, da mambobi 10 ne suka shigar da ƙorafin abin da Ciyaman ɗin yake aikata wa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Honorabul Yusuf Isma'il Falgore, ya ce ana zargin ciyaman ɗin da yanke hukunci bisa ra'ayin kansa ba tare da tuntuɓar kansiloli ba.

Yadda majalisar Kano ta bi matakan bincike

Bayan samun waɗan nan ƙorafe-ƙorafe kan Ciyaman ɗin, majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin wucin gadi, wanda ta ɗora wa alhakin gudanar da bincike don tabbatar da zargin.

Ta kuma bai wa kwamitin wa'adin kwanaki 60 watau tsawon watanni biyu ya kammala bincike kuma ya kawo mata rahoton abubuwan da ya gano.

Daga nan sai majalisar ta umarci mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ya karɓi ragamar harkokin mulkin Gwale na tsawon watanni 3 gabanin kammala bincike, rahoton Nigerian News.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Neman Dawowa Ɗanye, Tsagin Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi Ga Wike

An Kama Fasto Bisa Zargin Dambarar Wata Mata Naira Miliyan 1.6 a Jihar Ondo

A wani labarin na daban kuma Jami'an tsaron rundunar NSCDC sun damƙe wani Malamin addini bisa zargin zambatar wata mata kuɗi N1.67m a jihar Ondo.

Kakakin hukumar ya bayyana cewa Faston ya damfari wasu mutane da dama da ba a san yawansu ba a lokuta daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262