Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar Tarayya Na NNPP, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC a Kano

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar Tarayya Na NNPP, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC a Kano

  • Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisun tarayya ta ayyana Munir Babba Danagudi na APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Kumbotso
  • Hukuncin da kotun ta yanke ya kuma tsige dan majalisar NNPP, Idris Dankawu daga kujerarsa a majalisar wakilai
  • Kotu ta kama Dankawu da laifin kirkirar sakamakon jarrabawarsa na WAEC wanda ya gabatar a zaben

Jihar Kano - Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisun tarayya ta tsige Idris Dankawu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) daga kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kumbotso ta jihar Kano.

Channels Tv ta rahoto cewa kotun ta tsige Dankawu kan kirkirar takardar jarrabawarsa ta WAEC wacce ya gabatar domin shiga zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Ahaf: Rashin Gaskiya Ta Sa Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP a Kano, An Ba Dan Takarar APC

Kotun zabe ta tsige Dankawu daga kujerar dan majalisar tarayya daga Kano
Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Dan Majalisar Tarayya Na NNPP, Ta Bai Wa Jam'iyyar APC a Kano Hoto: Idris Dankawu/Muhsin Muhammad Aliyu
Asali: Facebook

Kotun zabe ta tsige dan majalisar NNPP kan kirkirar satifiket din makaranta

Munir Babba Danagudi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya yi takara da Dankawu ya shigar da kara kotu yana mai zargin cewa Dankawu ya yi amfani da satifiket din bogi wajen samun gurbin karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli, Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake zartar da hukunci kan shari'ar, Mai shari'a I.P. Chima ya bayyana cewa Idris Dankawu na NNPP ya kirkiri takardar WAEC din shi saboda haka an soke zabensa.

Kotun zaben ta kuma umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bai wa Dankawu a baya, rahoton Daily Post.

Hakazalika, kotun zaben ta ayyana Danagudi a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Kumbotso da aka yi a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Kotu ta tsige fitaccen dan majalisar wakilai na PDP, ta fadi dalili

Mai shari’a Chima ya jaddada bin doka na kotun zaben, inda ya ce:

“Bayan gamsuwa da tanadin dokar, muna masu ayyanawa tare da mayar da Munir Babba Danagudi a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Kumbotso."

Abia: Kotu ta tsige 'yan majalisun tarayya biyu na LP, ta ba APC da APGA nasara

A wani labari makamancin wannan, otun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen yan majalisun tarayya (NASS) ta tsige ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Arochukwu/Ohafia, Ibe Okwara, na Labour Party (LP).

Channels tv ta tattaro cewa Kotun zaɓen NASS mai zama a Umuahia, babban birnin jihar Abiya ta yanke wannan hukunci ne ranar Litinin, 11 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng