Zaben 2023: Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Party Da Kotu Ta Kora Ya Yi Martani

Zaben 2023: Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Party Da Kotu Ta Kora Ya Yi Martani

  • Injiniya Chijioke Stanislaus Okereke ya yi magana kan hukuncin kotun zaɓe mai zamanta a Enugu wanda ya ƙwace nasararsa
  • Okereke ya nuna takaicinsa kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta yanke akan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓe
  • Ɗan siyasar ya sanar da cewa ya yanke shawarar tunkarar kotun ɗaukaka ƙara domin kare amanar da mutane suka ba shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Enugu, jihar Enugu - Injiniya Chijioke Stanislaus Okereke, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Aninri, Awgu, Oji-River ya bayyana cewa zai garzaya kotun ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.

Kotun sauraron ƙararrakin ƴan majalisar tarayya mai zamanta a birnin Enugu, ta bayyana Anayo Onwuegbu, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin halastaccen ɗan majalisar da zai wakilci Aninri/Awgu/Oji River a majaisar wakilai ta 10.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Dan majalisar LP ya yi martani bayan kotu ta kwace kujerarsa
Okereke ya ce zai garzaya kotun daukaka kara Hoto: Hon. Engr. Chijioke Stanislaus Okereke - CSO
Asali: Facebook

"Za mu ɗaukaka ƙara", Okereke na LP

Kotun zaɓen ta buƙaci hukumar zaɓe ta INEC da ta ba shi satifiket ɗin lashe zaɓe a maimakon wanda tun da farko ta ba Okereke na jam'iyyar Labour Party (LP), wanda ta ce ya lashe zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake martani kan hukuncin kotun a cikin wata sanarwa wacce Legit.ng ta samu a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, Okereke ya yi amanna cewa hujjojin da suka gabatar a cikin ƙarar yakamata a sake duba su.

A kalamansa:

"A shirye mu ke mu bi duk matakan shari'a domin tabbatar da cewa an saurari muryoyin jama'a tare da tabbatar da nasarar abin da suka zaɓa."
"Dimokuraɗiyyar mu an gina ta ne akan tsarin ba al'umma ƴancin zaɓar waɗanda za su wakilce su, sannan aikin mu ne tabbatar da cewa mun kare wannan ƴancin.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Atiku Da Peter Obi Sun Bayyana Matakin da Zasu Ɗauka Bayan Ƙotun Zabe Ta Yanke Hukunci

"Ba mu kaɗai ba ne a cikin wannan gwagwarmayar, muna da goyon baya da addu'oin dubunnan waɗanda mu ke wakilta waɗanda suka yi amanna da abubuwan da mu ka gabatar musu a lokacin yaƙin neman zaɓe."

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Majalisar APC

A wani labarin na daban, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta tabbatar da nasarar Philip Agbese na jam'iyyar APC, mai wakiltar Ado/Okpokwu/Ogbadibo a jihar Benue.

Kotun ta yi fatali da ƙarrakin abokan takararsa na jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da Labour Party (LP) suka shigar suna ƙalubalantar nasararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng