Hukuncin Kotun Zabe: Shettima Ya Sake Shan Caccaka Kan Batun Yi Wa Atiku Ritaya
- Tsohon kakakin jam'iyyar APC, Kwamrae Timi Frank, ya caccaki mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima kan furucinsa game da yi wa Atiku Abubakar ritaya
- Shettima ya yi furucin ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja jim kadan bayan kammala shari'a a kotun zaben shugaban kasa
- Kwamrad Frank ya nuna rashin gamsuwarsa ga hukuncin kotun, yana mai bayyana shi a matsayin juyin mulkin bangaren shari'a a Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya sake shan caccaka kan furucin da ya yi cewa zai yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ritaya zuwa gidan gona bayan kotun zaben shugaban kasa ta yanke hukunci.
Da yake jawabi ga manema labarai a karshen zaman kotu a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, Shettima, ya bayyana Atiku a matsayin dattijon kasa da ake ganin mutuncinsa wanda bai cancanci ritaya a Dubai.
Hukuncin Kotun Zabe: Shettima Ya Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo, Ya Ce Zai Siya Masa Kaji Da Akuyoyi Ya Fara Kiwo
Ya ce:
"Ba za mu yi wa Atiku ritaya zuwa Dubai ko Morocco ba. Zan masa ritaya zuwa Fombina. Zan siya masa akuyoyi, kajin turawa da kaji masu kwai don ya shafe kwanakinsa yana kiwon shanaye da kaji.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Magana ta gaskiya, Atiku dattijon kasa ne. Kasar na bukatarsa."
A halin da ake ciki, Timi Frank, na hannun damar Atiku, ya mayar da martani kan jawabin Shettima, yana mai cewa Allah ne kadai zai iya yi wa ubangidan nasa ritaya.
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Frank ya ce:
"Ya kamata Shettima ya sani cewa wanda ke da Allah, kamar yadda aka cewa, shine mai rinjaye. Atiku yana da mafi rinjaye kuma wannan ne dalilin da yasa yan Najeriya basu yi farin ciki ko murnar tabbatarwa da aka yi ta juyin mulkin bangaren shari'a da PEPC ta yi na tabbatar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa."
Timi Frank ya ga laifin hukuncin kotun zabe
Kwamrad Frank ya bayyana hukuncin kotun a matsayin "juyin mulkin bangaren shari'a kan kasar Najeriya" kuma "kautan bauna kan mutanen."
Sai dai kuma ya bayyana cewa har yanzu bangaren shari'ar na da damar gyara sunanta da dawo da yardar mutane a kansu yayin da Atiku ya daukaka kara a kan hukuncin kotun a kotun koli.
Kwamrad Frank ya ce:
“Bangaren shari’a tayi amfani da damar wajen wanke kanta. Duk da ’yan Najeriya sun rasa kwarin gwiwa da fata kan tsarin shari’a, an sake ba su wata dama ko dai su ruguza Najeriya a karshe ko kuma su rubuta sunayensu da zinari ta hanyar yanke hukunci na rashin tsoro, jajircewa da gaskiya.”
Kotun zabe ta tsige dan majalisar tarayya na PDP a Bayelsa
A wani labarin, kotun sauraron kararrakin zabe da ke zama a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, ta soke zaben mazabar tarayya ta Sagbama/Ekeremor sannan ta tsige Hon Fred Agbedi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Kamar yadda AIT online ta rahoto, kwamitin kotun zaben ya umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta janye takardar sahidar cin zabe da ta bai wa Agbedi nan take.
Asali: Legit.ng