Jerin Sanatocin Jam’iyyar APC da Kotu Ta Kora Kafin a Cinye Albashin Wata 3 a Majalisa

Jerin Sanatocin Jam’iyyar APC da Kotu Ta Kora Kafin a Cinye Albashin Wata 3 a Majalisa

  • Jam’iyyar APC mai-mulki ta samu rinjaye a Majalisar dattawa a babban zaben bana da aka shirya
  • Da aka tafi kotun sauraron korafin zaben 2023, sai ga shi APC ta rasa wasu daga cikin kujerunta
  • Kotu ta tsige wasu Sanatocin na Jam’iyya mai-ci, hakan ya ba jam’iyyun adawa karin wuri a majalisa

Abuja - A rahoton nan, abin da Legit.ng Hausa tayi shi ne bibiyar shari’o’in zaben 2023, aka dauko wuraren da jam’iyyar APC ta rasa sanatocinta.

Sanatoci
Natasha Akpoti-Uduaghan za ta tafi Majalisa Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

A mafi yawan shari’o’in da aka yi zuwa yanzu, wadanda ke kan mulki ne su ke cigaba da rike kujerarsu, amma wasu ba su yi wannan dacen ba.

Ga Sanatocin da zuwa yanzu kotu ta tsige su ko kuma ta bukaci a sake gudanar da wani zaben:

1. Sanata Thomas Onowakpo (APC)

A makon nan kotun sauraron korafin zaben majalisar tarayya da ke zama a Delta ya tsige Thomas Onowakpo a matsayin Sanatan Delta ta Kudu.

Kara karanta wannan

Karatun Karshe da Sheikh Abubakar Giro Argungun Ya Yi Kafin Ya Komawa Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta ce a sake shirya sabon zabe nan kwanaki 90 a sakamakon da ‘dan takaran PDP, Thomas Onowakpo ya shigar, ya zargi INEC da saba doka.

2. Sanata Jibrin Isa (APC)

Kotun karar zabe da ke zama a Lokoja ya kori Jibrin Isah daga majalisar dattawan Najeriya bayan sauraron karar da ‘dan takaran PDP ya shigar.

PDP ta yi ikirarin an taba kuri’u 59, 730 saboda haka za a sake gudanar da zabuka a wasu rumfuna 94 da aka soke kuri’unsu a mazabar gabashin Kogi.

3. Abubakar Sadiku-Ohere (APC)

Mai shari’a Kemakolam Ojiako ya tunbuke Sanata Abubakar Sadiku-Ohere daga kujerar da yake kai a APC, ya ba Natasha Akpoti-Uduaghan nasara.

Alkalin kotun zaben ya zartar da hukunci cewa Natasha Akpoti-Uduaghan ce asalin Sanatar Kogi ta tsakiya ba Sanatan na APC da INEC ta ba nasara ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke, Ya Fada Wa Atiku da Obi Mafita

Tinubu ya doke PDP da LP a Kotu

Ana da labari Mai girma shugaban Najeriya watau Bola Tinubu ya yi farin ciki da hukuncin da kotu ta zartar na ba shi nasara a zaben shugaban kasa.

Bola Tinubu ya jinjinawa alkalan sannan ya bukaci a hada-kai domin jagorancin mutanen Najeriya wajen cika alkawuran da ya dauka lokacin kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng