Atiku Abubakar Ya Yi Jimamin Rasuwar Sheikh Giro Argungu
- Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya miƙa saƙon ta'aziyyar Giro Argungu
- Atiku ya yaba da irin gudummawar da shahararren malamin ya bai wa addinin Musulunci a lokacin rayuwarsa
- Ya ce za a dade ana ana amfana da koyarwa malamin ta fuskar zaman lafiya da lumana a tsakanin al'ummar musulmi
FCT, Abuja - Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu da Allah ya yi wa rasuwa.
Atiku ya fitar da sakon ta'aziyyar ta sa ne a cikin wani rubuto da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba.
Atiku ya yi jimamin rasuwar Giro Argungu
Atiku ya bayyana alhininsa na rashin Sheikh Giro Argungu da aka yi, wanda ya rasu bayan gajeruwar jinya a garin Argungu da ke jihar Kebbi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Atiku ya ce Sheikh Giro na daga cikin manyan-manyan malaman addinin Musulunci da ake girmamawa a Najeriya da Yammacin Afrika baki daya, saboda irin gudummawar da ya ba da.
Ya ƙara da cewa za a dade ana tuna gami da cin moriyar karantarwarsa wacce ta yi tasiri sosai wajen samuwar zaman lafiya da lumana a tsakanin al'umma.
Wani bangare na Kalaman Atiku na cewa:
“A madadin iyalina, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan malamin, al'ummar Musulmi da ma Najeriya baki ɗaya.”
Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sheikh Giro Argungu
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan saƙon ta'aziyya da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike ga iyalan marigayi Sheikh Giro Argungu da ya rasu ranar Laraba.
Tinubu ya bayyana rasuwar Giro a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Hadimin Shugaba Tinubu Cif Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Atiku ya musanta batun taya Tinubu murna
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan musanta batun taya Tinubu murnar nasara a kotun zabe da aka ce Atiku ya yi.
Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce dan takararsu za su daukaka kara.
Asali: Legit.ng