Kotun Zabe Ta Tsige Sanatan Delta Ta Kudu, Ta Yi Umurnin Sake Zabe Cikin Kwana 90

Kotun Zabe Ta Tsige Sanatan Delta Ta Kudu, Ta Yi Umurnin Sake Zabe Cikin Kwana 90

  • Kotun sauraron korafe-korafen zaben 'yan majalisar tarayya a Delta ta tsige sanatan APC na Delta ta kudu daga kujerarsa
  • Da take yanke hukunci a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, kotun ta ba da umurnin janye takardar shaidar cin zaben Sanata Thomas Onowakpo
  • Ta kuma yi umurnin sake zabe a karamar hukumar Warri ta kudu cikin kwana 90

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Delta - Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisar tarayya da ke zama a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta tsige dan majalisar tarayya mai wakiltan yankin Delta ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Thomas Onowakpo.

Kotun zabe ta tsige Sanata Thomas Onowakpo daga kujerarsa
Kotun Zabe Ta Tsige Sanatan Delta Ta Kudu, Ta Yi Umurnin Sake Zabe Cikin Kwana 90 Hoto: Delta South Senatorial District
Asali: Facebook

Kotu ta yi umurnin janye takardar shaidar cin zaben Onowakpo

Dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, Mista Michael Diden, ya tunkari kotun zabe da korafinsa na neman a soke nasarar dan takarar jam'iyyar APC, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa

Ya yi korafin cewa hukumar zaben bata bi dokar zabe ba kafin ta ayyana APC a matsayin wacce ta lashe zaben.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabar kotun zaben, Mai sharia Catherine Ogunsola ta bayyana cewa za a janye takardar shaidar cin zaben Onowakpo.

Kotun zaben ta kuma yi umurnin gudanar da sabon zabe a karamar hukumar Warri ta kudu da ke jihar cikin kwana 90, rahoton Vanguard.

Da yake magana jim kadan bayan yanke hukunci, lauyan INEC, ya ce za su yi nazari a kan hukuncin, yana mai cewa har yanzu suna da damar daukaka kara.

Ya ce:

"An yanke hukunci kuma za mu je gida sannan mu yi nazarin hukuncin. An bukaci da mu janye takardar shaidar cin zabensa sannan mu gudanar da zaben cike gurbi cikin kwana 90."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben da Ɗan Takarar NNPP Ya Samu Nasara a Jihar Kano

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar Abdulmumini Jibrin a matsayin dan majalisar tarayya

A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisar tarayya da ke zama a Kano ta yanke hukunci cewa Muhammad Sa'id Kiru na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya gaza gabatar da shaidu da za su tabbatar da an tauye masa hakki a yayin zaben 2023.

An rahoto cewa kotun zaben ta kuma yi watsi da karar da ya shigar kan nasarar Abdulmumini Jibrin na jam'iyyar NNPP a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng