Kotun Zabe: Makomar Najeriya Tana Hannunku, Fasto Adewale Giwa Ya Fadawa Alkalai

Kotun Zabe: Makomar Najeriya Tana Hannunku, Fasto Adewale Giwa Ya Fadawa Alkalai

  • Shugaban cocin ‘Awaiting The Second Coming Of Christ Ministries’, Adewale Giwa ya yi tsokaci kan shari'ar zaɓe
  • Ya nemi alƙalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen da su yanke hukunci bisa gaskiya da adalci
  • Shawarar ta Giwa na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ƙararrakin zaɓen ke shirin yanke hukunci kan karar Atiku da Obi a kan Tinubu

Akure, jihar Ondo - Babban limamin cocin ‘Awaiting The Second Coming Of Christ Ministries’ Adewale Giwa, ya shawarci alƙalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, kan cewa su duba abinda 'yan Najeriya ke so.

Giwa wanda ya bayyana hakan a garin Akure da ke jihar Ondo, ya shawarci alƙalan da su yi abinda ya dace wajen yanke hukunci kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Fasto ya bai wa alƙalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓe shawara
Fasto Adewale Giwa ya nemi alƙalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓe su yi hukunci bisa gaskiya da adalci. Hoto: Segun Adeyemi
Asali: Original

Giwa ya ce makomar Najeriya na hannun alƙalan kotun zaɓe

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Tsaffin Tsagerun Neja Delta Suka Dira Kotun Zaben Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

A ranar Larabar nan 6 ga watan Satumba ne dai kotun zaɓen za ta yanke hukunci kan ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A dalilin hakan ne Adewale Giwa ya shawarci kwamitin mutum biyar da mai shari'a Haruna Tsammani ke jagoranta, da su guji maimaita tarihin shari'o'in da suka gudana a shekarun baya.

Ya bayyana cewa makomar Najeriya na maƙale a hannunsu kan irin hukunci da suka yanke a shari'ar da za ta gudana a yau.

Kada ku yi kuskuren juyar da abinda 'yan Najeriya ke so

Giwa ya ƙara da cewa duk da ya san cewa shawarar ta sa ta zo ne a ƙurarren lokaci, ya shawarci alƙalan da su tabbatar da cewa ba su sanar da akasin abinda 'yan Najeriya ke tsammani ba.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Babban Lauya Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Kotun Zaben Shugaban Kasa Yanke Hukunci a Ranar Laraba

Ya roke su da su tabbatar da cewa duk wani hukunci da suka riga suka yanke wanda suke shirin sanarwa a yau Laraba, ya kasance na adalci da zai yi wa 'yan ƙasa daɗi.

Tun bayan ayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi, Atiku Abubakar na PDP, da Peter Obi na LP suke ƙalubalantar nasarar ta sa.

Jigon APC ya fadi wanda zai yi nasara a kotun zabe

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan iƙirarin da wani jigo a jam'iyyar APC Tolu Bankole ya yi dangane da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke.

Ya bayyana cewa shi yana da tabbacin cewa kotun za ta tabbatar da nasarar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng