Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Fasto Kingleo Elijah Ya Ce Wasu Za Su Sharɓi Kuka Bayan Hukunci

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Fasto Kingleo Elijah Ya Ce Wasu Za Su Sharɓi Kuka Bayan Hukunci

  • Fasto David Kingleo Elijah, na Cocin ‘Glorious Mount of Possibility’, ya hasaso yadda za ta kaya a kotun zaɓe
  • Ya bayyana cewa wasu daga cikin magoya bayan Atiku, Obi da Tinubu za su yi kuka, yayinda wasu kuma za su dara
  • Faston ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi fatan Allah ya ba su wanda zai fi zama alkhairi ta fuskar tsaro da zaman lafiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fasto David Kingleo Elijah na Cocin ‘Glorious Mount of Possibility’, ya bayyana abinda zai biyo bayan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe za ta yanke na shari'ar Atiku, Peter Obi da Tinubu.

Kotun zaɓen dai ta tsayar da ranar Laraba, 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ingancin nasarar Bola Tinubu ko akasin hakan.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi Da Tinubu: Jigon PDP Ya Ce Bai Dace Kotu Ta Ayyana Wanda Ya Yi Nasara Ba, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi

An fadi abinda zai faru bayan hukuncin kotun zabe
An fadi abinda zai faru bayan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi
Asali: Twitter

Wasu za su sha kuka bayan hukuncin kotu

A wani bidiyo da ya wallafa a tasharsa ta YouTube, faston ya ce wasu daga cikin magoya bayan 'yan takarar uku za su sharɓi kuka, yayinda wasunsu kuma za su yi dariya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kingleo Elijah ya ce babban abinda ya kamata 'yan Najeriya su yi shi ne roƙon Allah ya ba su wanda zai fi zama alkhairi ta fuskar samar da tsaro da zaman lafiya.

Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, da Peter Obi na jam'iyyar Labour ne dai ke kan gaba wajen ƙalubalantar nasarar lashe zaɓen da Shugaba Tinubu ya yi a gaban kotu.

Bode George ya nemi kotu ta sanya INEC sake zabe

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan tsokacin da jigon jam'iyyar PDP, Cif Olabode George ya yi kan shari'ar zaben shugaban kasa da za a yanke hukuncinta ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

Ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda kotunan Najeriya ke taka muhimmiyar rawa wajen bayyana ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓe.

Bode George ya buƙaci kotun sauraron ƙararrakin zaɓen da ta yi hukunci cikin adalci, ko ma ta bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), damar sake gudanar da sabon zabe.

Jami'an tsaro sun gargadi masu son tada husuma

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da jami'an tsaro suka yi wa masu son tada husuma dangane da hukuncin da kotun zaɓe za ta yanke ranar Laraba.

Jami'an sun bayyana cewa ba za su lamunci duk wani nau'i na zanga-zanga ko tayar da hankulan jama'a ba, kuma za su ɗauki mataki kan duk wanda ya aikata hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng