Atiku, Obi Da Tinubu: Bode George Ya Ce Bai Kamata Kotu Ta Sanar Da Wanda Ya Yi Nasara a Zaɓen 2023 Ba

Atiku, Obi Da Tinubu: Bode George Ya Ce Bai Kamata Kotu Ta Sanar Da Wanda Ya Yi Nasara a Zaɓen 2023 Ba

  • Jigon jam'iyyar PDP, Olabode George, ya aike da muhimmin sako ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓe
  • Ya nuna damuwarsa kan rawar da ma'aikatun shari'a ke takawa wajen bayyana ɗan takarar da ya lashe zaɓe
  • Ya bukaci kotun ta yi adalci wajen yanke hukuncin, ta kuma bai wa INEC damar sake gudanar da zabe idan akwai buƙatar hakan

Ikoyi, jihar Legas - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Olabode George, ya yi tsokaci kan rawar da kotunan Najeriya ke takawa wajen tabbatar da ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓe.

Ya yi kira ga kotun zaɓe da ta yi ƙoƙarin yin adalci wajen yanke hukunci ta hanyar bai wa mutane ainihin abinda suka zaɓa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Bode George ya fadi abinda ya kamata kotun zaɓe ta yi
Bode George ya bukaci kotun zaɓe ta bai wa INEC umarnin sake gudanar da sabon zaɓe. Hoto: Chief Olabode George, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

George ya ce ba sanar da wanda ya lashe zaɓe ya kamata a yi ba

Kara karanta wannan

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Jami'an Tsaro Sun Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Gabanin Yanke Hukunci

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe dai za ta yanke hukuncinta kan cewa Bola Tinubu ne ya lashe zaɓen 2023 na shugaban ƙasa ko akasin haka a ranar Laraba mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake mayar da martani kan batun, Bode George ya ce ba sanar da wanda ya lashe zaɓen ya kamata kotun ta yi ba, kamata ya yi ta bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), damar sake sabon zaɓe.

A rahoton Business Day, Bode George ya ce kotu wani ɓangare ne na gwamnati, inda yake ganin bai dace ace ita ce za ta faɗawa al'umma wanda ya lashe zaɓe ba.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi idan kotun ta fahimci akwai matsaloli a zaɓen, ta ba da umarnin a je a sake gudanar da shi don kore tantama.

Kara karanta wannan

Manya-manyan Bukatu 5 Da Peter Obi Ya Mikawa Kotu Kan Shari'arsa Da Bola Tinubu

Jami'an tsaro sun gargaɗi masu shirin gudanar da zanga-zanga

A baya Legit.ng ta kawo wani rahoto na gargaɗin da jami'an tsaron Najeriya suka yi wa masu yunkurin gudanar da zanga-zanga saboda hukuncin da kotun zaɓe za ta yanke ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Jami'an 'yan sanda da na soji sun bayyana cewa ba za su lamunci duk wani nau'i na zanga-zanga ba, domin sun fahimci ana son fakewa da ita domin tayar da zaune tsaye.

Jami'an sun ba da tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen daƙile shirin duk masu neman tayar da husuma.

Bukatu 5 da Peter Obi ya miƙawa kotun zaɓe

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wasu manyan-manyan buƙatu da ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Labour, Peter Obi ya mikawa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Daga cikin buƙatun da Peter Obi ya shigar gaban kotun a shari'arsa da Shugaba Bola Tinubu akwai roƙon kotu ta hannanta shugabancin Najeriya gareshi.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Karamar Hukumar Jihar APC da Ta Tsare, Bayanai Sun Fito

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng