Gwamna Obaseki Ya Rantsar da Sabbin Ciyamomi 18 da Suka Ci Zabe a Edo
- Gwamna Obaseki ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar Edo bayan sun samu nasara a zaɓe
- A ranar Asabar da ta gabata aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar kuma jam'iyyar PDP ta samu galaba
- Amma jam'iyyar APC ta maida martani da cewa babu wani zaɓe da ya gudana a Edo ranar Asabar
Edo - Gwamnan jigar Edo, Godwin Obaseki, ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 18 da suka samu nasara a zaben ranar Asabar da ta gabata.
Gwamna Obaseki ya ɗauki wannan matakin na bai wa Ciyamomin rantsuwar kama aiki duk da kiraye-kirayen jam'iyyar APC na dakatar da bikin rantsarwan.
Godwin Obaseki ya bayyana cewa a tsanake PDP ta zaƙulo su ta tsayar da su takara kuma al'umma suka fito kwansu da kwarkwata suka kaɗa musu kuri'a, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Ya kuma nuna kwarin guiwar cewa sabbin shugabannin kananan hukumomin zasu haɗa kai da gwamnatin jihar Edo domin samar da shugabanci na gari ga al'umma.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A rahoton Vanguard, gwamna Obaseki ya ce:
"Na taya ku kamfe a kafatanin ƙananan hukumomin jihar nan, saboda haka ban yi mamakin nasarar da kuka samu ba, amma abinda ya bani sha'awa shi ne ƙaunar da mutane su ke wa PDP, kar ku basu kunya."
Obaseki ya roƙi Ciyamomin su maida hankali wajen bunƙasa yankunan da su ke jagoranta, sannan kuma su tabbatar da tsaftar mahalli.
Jam'iyyar APC ta maida raddi
Da yake maida martani, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Edo, Kanal David Imuse (mai ritaya) ya ce ba a gudanar da zaben kananan hukumomi ba a ranar Asabar.
Gwamnan ya ce:
“Abin da aka ce zabe ne ba komai bane illa yaudara, lamarin da ya jefa ‘yan Edo cikin rudani tare da sanya ayar tambaya kan ingancin hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Edo."
“Ba a gudanar da zaben kananan hukumomi ba, don haka babu wani sakamako da ya kamata hukumar EDSIEC ta fitar. Kada a yi yunkurin rantsar da wani ko wasu a matsayin Ciyamomi ko kansiloli."
"APC na kira ga duk masu ruwa da tsaki, kungiyoyin farar hula, da sauran jama'a, da su lura da wannan mummunar ta'asa, su hada kai da mu wajen neman adalci ga al'ummar jihar Edo."
Gwamnan Delta Ya Nada Abokin Adawarsa Na NNPP a Matsayin Hadimi
A wani rahoton kuma Gwamnan jihar Delta na jam'iyyar PDP ya naɗa sabbin masu ba shi shawara ta musamman guda 9.
Sakataren gwamnatin jihar, Kingsley Emu, ya bayyana cewa gwamnan ya naɗa abokin gwabzawarsa a zaben da ya gabata a muƙami mai girma.
Asali: Legit.ng