Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Shugaban Karamar Hukuma Na Jihar Ogun
- Hukumar tsaro DSS ta saki shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas, wanda ta tsare a hannu tun ranar Jumu'a
- Jim kaɗan bayan ya shaƙi iskar yanci, Honorabul Wale Adedayo, ya ce DSS ta gayyace shi ne kan wasu ƙorafe-ƙorafe da aka kai mata
- Adedayo ya shiga hannun DSS ne bayan ya yi zargin cewa gwamna Abiodun na Ogun na karkatar da dukiyar talakawa
Ogun - Dakataccen shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun, Honorabul Wale Adedayo, wanda hukumar tsaron farin kaya ta tsare tun ranar Jumu'a ya shaƙi iskar 'yanci.
Honorabul Adedayo, shi ne ya tabbatar da haka yayin zanta wa da wakilin jaridar Punch a Abeokuta, babban birnin Ogun jim kaɗan bayan jami'an DSS sun sako shi ranar Litinin.
Ya ce hukumar DSS ta gayyace shi ne bisa ƙorafin da aka shigar gabanta cewa ya yi wasu kalaman tunzura mutane wanda ka iya zama barazana ga zaman lafiya, Pulse ta tattaro.
Dakataccen Ciyaman ɗin ya bayyana cewa ya faɗa wa hukumar cewa ko kaɗan bai yi wasu kalaman tunzura al'umma ba illa zargin da ya yi cewa ciyamomi ba su samu ko kwandala daga gwamnatin jiha ba a shekara 2.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce yana nan kan bakarsa kan lamarin kuma ya tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya zai ƙalubalanci dakatarwan da aka masa, wacce ya ayyana ba kan ƙa'ida ba.
Meyasa ya rubuta takardar ƙorafi kan gwamna?
Adedayo ya ce ya rubuta wasikar ƙorafi kan Gwamna Dapo Abiodun zuwa ga tsohon gwamnan jihar, Cif Olusegun Osoba, tare da goyon bayan sauran shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ogun.
Amma a cewarsa, ya yi mamakin yadda baki ɗayansu suka juya baya kan yaƙin da suka fara da nufin tabbatar da shugabanci na gari a matakin da ya fi kusa da jama'a.
Idan zaku iya tunawa, ciyaman din da aka dakatar ya rubuta wasiƙa ga Mista Osoba, inda ya ce gwamnan jihar, Dapo Abiodun na karkatar da haƙƙin al'umma, Channels tv ta ruwaito.
Gwamnatin Tarayya Zata Gana da Kungiyar Kwadago Kan Batun Yajin Aiki
A wani labarin na daban Gwamnatin tarayya ta fara yunkurin dakatar da ƙungiyoyin kwadago daga shiga yajin aikin gargaɗi na kwana 2.
Ministan kwadago da samar da ayyuka, Simon Lalong ya roƙi NLC da kawayenta kada su tsunduma yajin aikin domin zasu maida hannun agogo baya.
Asali: Legit.ng