Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Ranar Laraba

Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu: Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Ranar Laraba

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci kan shari'ar Atiku, Obi da Tinubu cikin satin nan
  • Kotun zaɓen ta tsayar da ranar Laraba, 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta bayyana sakamako
  • A ranar ne Atiku, Tinubu da Peter Obi za su san makomarsu dangane da zaɓen watan Fabrairu da ya gabata

FCT, Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen da ke tsakanin Atiku Abubakar, Peter da Shugaba Bola Tinubu.

Kotun zaɓen za ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba da muke ciki kamar yadda gidan talabijin na AIT ya ruwaito.

Kotun zabe za ta yanke hukunci ranar Laraba
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci ranar Laraba. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi
Asali: Facebook

Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar gwamnoni

Ana sa ran cewa kotunan zaɓen da ke a jihohin daban-daban na ƙasar nan ma za su sanar da hukunce-hukunce shari'o'in zaɓuƙan gwamna da suka gudana a jihohi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Tarzoma a Kasa, Ta Magantu Kan Masu Hannu a Ciki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun bayan sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe ne dai Atiku da Peter Obi ke ƙalubalantarsa a gaban kotu.

Sun yi iƙirarin cewa Tinubu bai cancanta ba, kuma zaɓen na sa da aka yi wanda ya kai ga ba shi nasarar zamowa shugaban ƙasa cike yake da kura-kurai.

Kotun za kuma ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da jam'iyyar APM ta shigar dangane da zaɓen duk a ranar Laraba.

An bukaci kotun zaɓe ta yi adalci wajen yanke hukunci

A wani rahoto mai alaƙa da wannan da Legit.ng ta yi a baya, wata kungiyar ta 'yan Najeriya da ta roƙi kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƙasa kan ta yi hukunci na adalci.

Ƙungiyar mai suna Coalition of Concerned Nigerians (CCN), ta bukaci kotun zaɓen ta yanke hukunci da zai yi wa 'yan ƙasa daɗi ba tare da nuna son rai ba.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu Da Obi Za Su San Makomarsu Yayin Da Kotun Zaɓe Ta Sanar Da Lokacin Yanke Hukunci

Shugaban LP ya ce Peter Obi zai kwace kujerar Tinubu

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan jawabin da shugaban jam'iyyar Labour Julius Abure ya yi na cewa Peter Obi zai dare kujerar Tinubu, wacce kotun ƙararrakin zaɓe za ta karɓa ta ba shi.

Abure ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattaunawa da wasu mazauna Najeriya a ƙasar Amurka, a yayin wata ziyara da ya kai mu su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng