Cikakken Sakamako: PDP Ta Lashe Dukan Zaben Kananan Hukumomi 18 a Jihar Edo
- A ranar Asabar, 2 ga watan Satumba ne aka gudanar da zabe a fadin kananan hukumomin jihar Edo
- Kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar da sakamako, PDP ce ta lashe gaba daya kujeru 18 a zaben kananan hukumomin
- Jam'iyyun All Progressives Congress (APC) da Labour Party (LP) ma sun shiga zaben amma sun tashi a tutar babu
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe zaben dukan kananan hukumomi 18 a jihar Edo a zaben kananan hukumomi da aka yi a ranar Asabar, 2 ga watan Satumba, kamar yadda sakamakon da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta saki ya nuna.
An gudanar da zaben a gaba daya kananan hukumomi 18 na jihar wanda ya kunshi Edo ta arewa, Edo ta tsakiya da Edo ta kudu, Channels TV ta rahoto.
Baya ga PDP, sauran manyan jam'iyyun siyasa da suka shiga zaben ciyamomi da kansiloli sun hada da All Progressives Congress (APC) da Labour Party (LP).
Ga cikakken sakamakon zaben a kasa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
PDP: 16077
APC: 2519
LP: 2536
1. Karamar hukumar Ovia ta kudu maso yamma
APC: 5361
LP: 3216
PDP: 10,721
2. Kamaramar hukumar Uhunmwode
Adodo O. Kenneth na PDP ya yi nasara
APC: 2317
LP: 1436
PDP: 15,615
3. Karamar hukumar Owan ta yamma
Ahonsi Dickson Idojemu na PDP ya lashe zabe
APC: 3825
LP: 2365
PDP: 13, 171
4. Karamar hukumar Akoko Edo
Tajudeen Alade Suleiman na PDP ya yi nasara
APC: 5369
LP: 2083
PDP: 21,417
5. Karamar hukumar Etsako ta gabas
Ato Benedicta ta PDP ta yi nasara
APC: 4076
LP: 1711
PDP: 16, 428
Yanzu Yanzu: Hukumar DSS Ta Tsare Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Zargi Gwamnan APC Da Karkatar Da Kudade
6. Karamar hukumar Etsako ta tsakiya
Obomigie Imokhae Solomon na PDP ya lashe zabe
APC: 7, 896
LP: 4, 606
PDP: 30, 594
7. Karamar hukumar Etsako ta yamma
Zimbiril Marvelous na PDP ya yi nasara
APC: 29, 445
LP: 23, 832
PDP: 98, 046
8. Karamar hukumar Ikpoba-Okha
DR. ERIC IYOBA OSAYANDE na PDP ya lashe zabe
APC: 3, 085
LP: 3, 857
PDP: 27, 768
9. Karamar hukumar Ovia ta arewa maso gabas
Collins Osamede Ogbewe na PDP ya lashe zabe
APC: 636
LP: 617
PDP: 4, 869
10. Karamar hukumar Igueben
Asueleme Clement na PDP ya lashe zabe
APC: 557
LP: 660
PDP: 5, 262
11. Karamar hukumar Esan ta tsakiya
Iyoha Paul of PDP ya lashe zabe
APC: 23, 885
LP: 14, 331
PDP: 47, 771
12. Karamar hukumar Orhionmwon
Ugiagbe Newman Oghomwen na PDP ya yi nasara
APC: 1616
LP: 1737
PDP: 14, 904
13. Karamar hukumar Esan ta yamma
Aigbogun O. Collins na PDP ya lashe zabe
APC: 1, 665
LP: 2, 183
PDP: 11, 963
14. Karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas
Imadegbeho Luis na PDP ya lashe zabe
APC: 1344
LP: 791
PDP: 16072
15. Karamar hukumar Esan ta arewa maso gabas
Inegbe Paul na PDP ya ci zabe
APC: 5550
LP: 3298
PDP: 20, 702
16. Karamar hukumar Owan ta gabas
Prince Aminu Kadiri na PDP ya ci zabe
APC: 12, 203
LP: 7695
PDP: 35, 380
17. Karamar hukumar Egor
Hon. Eghe Ogbemudia na PDP ya ci zabe
APC: 8, 308
LP: 10, 188
PDP: 70, 293
18. Karamar hukumar Oredo
Dr. Obaseki Tom Osazee na PDP ya yi nasara a zabe
Obaseki Vs Shaibu: Gwamnatin Edo Ya Sauya Wa Mataimakin Gwamna Ofis
A wani labarin, mun ji cewa biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin gwamnan Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, gwamnatin jihar ta fitar da ofishin mataimakin gwamnan daga gidan gwamnati.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa sabon ofishin mataimakin gwamnan yana lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, kusa da gidan gwamnatin jihar Edo.
Asali: Legit.ng