Ana Zanga-Zanga a Kano Kan ‘Shirin’ NNPP na Rusa Gadar da Sanatan APC ta Gina

Ana Zanga-Zanga a Kano Kan ‘Shirin’ NNPP na Rusa Gadar da Sanatan APC ta Gina

  • A lokacin da wata gada ta ruguje a Gwarzo, mazauna sun tuntubi Barau Jibrin domin ya taimaka masu
  • Nan ta ke mataimakin shugaban majalisar ya gyara gadar, hakan ya fusata gwamnatin NNPP mai ci
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce Sanata Jibrin bai nemi izini kafin ya yi garajen sake gina gadar ba

Kano - Mazauna garin Gwarzo a Arewacin jihar Kano su na Allah wadai da abin da su ka kira yunkurin gina wata gada da ‘dan majalisar APC ya gina.

Premium Times ta ce kwanakin baya ruwa ya share wata gada da ke Gwarzo, nan take al’ummar yankin su ka nemi taimakon Sanatansu, Barau Jibrin.

Kafin a ce kobo, Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa kuma mataimakin shugaban majalisa ya yi sanadiyyar da aka gyara muhimmiyar gadar.

Kara karanta wannan

Za A Iya Binciken Buhari Da Tsofaffin Shugabanni, A Kuma Canzawa Najeriya Sabon Suna

NNPP.
Magoya bayan NNPP a Kano Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Aiki har ya kammala a Kano

A ranar Juma’a aka kammala aikin gadar, Jibrin shi kadai ne Sanatan APC a majalisa daga Kano, watakila abin da ya faru bai yi wa NNPP mai mulki dadi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani direba mai suna Sule Wanzom, ya shaidawa jaridar cewa a ranar Juma’ar nan mazauna garin Gwarzo su ka fara zanga-zanga da jin take-taken gwamnati.

Ana kishin-kishin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na so ta ruguza gadar domin ta gina wanda ya fi shi kyau, har ranar Asabar zanga-zangar ba ta tsaya ba.

An kunya mataimakin Gwamna?

Wanzam ya ce gadar ta na da matukar muhimmanci a yankin kuma ta na kai wa har kauyen mataimakin gwamna mai-ci, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Gadar ta jona da gidan Aminu Abdussalam Gwarzo wanda hakan ya jawo ‘yan jam’iyyarsa (New Nigeria People Party) a kauyen su ka ji babu dadi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bayyana Shirinsa Na Samar da Attajiran Masu Kuɗi 150 a Jiharsa, Ya Ce In Sha Allah

Mazauna su na da ra’ayin cewa sabanin siyasa ya jawo ake so a ruguza wannan aiki ba komai ba, ‘Yan jam’iyyar APC sun nuna ba za su amince a rusa ba.

Abin da gwamnatin Abba ta fada

Marwan Ahmad wanda shi ne Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, ya ce ba a yanke hukunci a game da abin da ya dace ayi wa wannan gada ba tukuna.

Injiniya Ahmad ya ce kyau Sanata Jibrin ya fara neman izini kafin yin gyaran domin gadar ta na kan hanyar gwamnatin jiha ne ba gwamnatin tarayya ba.

Kwamishinan ya ce gwamnatin Abba ta bi ka’idojin aiki, an kammala komai kurum sai aka ji Sanatan ya yi gyaran, ba tare da ya nemi umarnin hukuma ba.

Rusau a Kano

Tun da Abba Kabir Yusuf ya shiga ofis ake yi masa zargin kokarin ganin ya shafe tarihin da Abdullahi Ganduje ya bari a lokacin da ya yi mulkin Kano.

Da ya hadu da Mai martaba Aminu Ado Bayero, sabon Gwamnan na jihar Kano ya ce yana rusa gine-gine ne saboda tun farko an saida filaye ba kan ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng