Zan Tabbatar Da APC Ta Kwace Mulki a Jihar Rivers, Ganduje Ya Ya Bugi Kirji Game Da Zabe Mai Zuwa
- Shugaban APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai kwace mulki a jihar Rivers ta hanyar hada kan ‘yan jam’iyyar
- Wata tawaga ta bayyana gwarin gwiwa da kuma jajircewar Ganduje wajen tabbatar da APC ta yi nasara a jihohin kasar
- Wannan na zuwa ne bayan da aka bayyana Ganduje a matsayin sabon shugaban APC na kasa bayan hawan Tinubu mulki
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi jam’iyyar PDP da ke shirin karbe jihar Rivers mai arzikin man fetur.
Ganduje ya yi wannan gargadin ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar gangamin Sanata Magnus Abe a ofishinsa da ke sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
Da yake gargadin jam’iyya mai mulki a jihar kana bin da ke tafe, tsohon gwamnan na Kano ya ce da yarjejeniyar manyan tubalan APC guda uku a jihar nan ba da jimawa ba jam’iyyar mai mulki a jihar za ta tattara kwamutsanta zuwa wajen gidan gwamnati.
A cewar shugaban jam’iyyar APC:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yanzu mun kawo karshen matsalar da ake fama da ita a jam’iyyar APC a jihar Rivers, domin a yanzu manyan tubala uku sun hada kai domin gina APC da muka sani a jihar Rivers.”
APC na neman wargajewa a baya a Rivers
Jagoran tawagar, Sanata Wilson Ake, ya bayyana yabonsa ga kwarin gwiwar da shugaban jam’iyyar na kasa yake dashi na hada kan jam’iyyar, musamman a jihar Rivers da ya ce ta fuskanci kalubale da dama da ke haifar da rashin jituwa da kuma neman wargajewa.
Ake ya tabbatarwa da shugabannin jam’iyyar APC shirin goyon bayan duk wani yunkuri na sake gina jam’iyyar a Rivers.
Ya yi nuni da cewa tawagar Magnus Abe ta yi aiki domin nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma tana burin karfafa da inganci a nan gaba.
Ganduje ya yi fatatta a APC
A wani labarin, jam'iyyar APC a Osun ta kori mambobinta 84 wadanda ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola.
Shugaban APC a Osun, Sooko Lawal, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, jaridar PM News ta rahoto.
A cewar sanarwar, ana zargin masu biyayya ga Aregbesola 84 da cin dunduniyar jam'iyya.
Asali: Legit.ng