Nadin Mukamai: Abba Gida Gida Ya Jawo Matasa 44, Ya Sakala a Ma’aikatun Kano
- Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin SSR da SR da za su rika aiki a ma’aikatun gwamnatin Kano
- Wadannan wakilai wanda da-dama matasa ne su na da nauyin sanar da abin da ake yi a ma’aikatu
- Sanarwar nadin mukaman ta fito daga ofishin abban sakataren yada labarai, Sanusi Dawakin Tofa
Kano - Abba Kabir Yusuf ya dauko matasa ya ba su wani mukami da aka kira SSR da SR watau masu tattara rahotanni na musamman daga MDAs.
Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwa a shafinsa a matsayinsa na babban sakataren yada labaran Mai girma gwamnan Kano.
Wadannan masu dauko rahoto za su yi aiki a ma’aikatun gwamnati da ake da su a Kano. Ga sunayensu kamar yadda aka sanar a ranar Juma’a:
Sababbin SR da SSR da ma'aikatunsu a Kano
1. Abba Zizu, Babban mai dauko rahoto, aikin gona
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Isma’il Alkassim, Mai dauko rahoto, aikin gona
3. Musa Garba (Jikan Oga), Babban mai dauko rahoto, Kasafin kudi da tsare-tsare
4. Bilal Musa Bakin Ruwa, Mai dauko rahoto, Kasafin kudi da tsare-tsare
5. Auwal Dan-Ayagi, Babban mai dauko rahoto, Masana’antu da kasuwanci
6. Usman Abubakar Haske, Mai dauko rahoto, Masana’antu da kasuwanci
7. Auwalu Yau Yusuf, Babban mai dauko rahoto, Al’adu da Bude ido
8. Kamal I.G Kawaji, Mai dauko rahoto, Al’adu da Bude ido
9.Kwamred Hayatu Tanimu, Babban mai dauko rahoto, Ilmi
10. Usman Ibrahim, Mai dauko rahoto, Ilmi
11. Mahmud Ali Yakasai, Babban mai dauko rahoto, muhalli
12. Rahma Abdullahi, Mai dauko rahoto, muhalli
13. Sani Umar, Babban mai dauko rahoto, tattalin arziki
14. Abdulrahman Gama, Mai dauko rahoto, tattalin arziki
15. Aliyu Kwankwason Dorayi, Babban mai dauko rahoto, lafiya
16. Zainab Muhammad, Mai dauko rahoto, lafiya
17. Nuhu Dambazau, Babban mai dauko rahoto, Ilmi mai zurfi
18. Zainab Musa Aujara, Mai dauko rahoto, Ilmi mai zurfi
19. Yakubu Umar, Babban mai dauko rahoto, Yada labarai
20. Ibrahim Yusha’u, Mai dauko rahoto, Yada labarai
21. Amir Abdullahi Kima, Babban mai dauko rahoto, Shari’a
22. Mahmud Mahmud Dala, Mai dauko rahoto, Shari’a
23. Mustapha R. Mahmud, Babban mai dauko rahoto, Tsarin Filaye da Safayo
24. Nanu Kankarofi, Mai dauko rahoto, Tsarin Filaye da Safayo
25. Khatimu Kul-Kul, Babban mai dauko rahoto, Kananan hukumomi
26. Aisha Auwal, Mai dauko rahoto, Kananan hukumomi
27. Kamal Yakasai, Babban mai dauko rahoto, Kula da ayyuka
28. Ibrahim M. Alliya, Mai dauko rahoto, Kula da ayyuka
29. Sunusi Ma’azu, Babban mai dauko rahoto, Harkokin Addini
30. Bashir Aliyu, Mai dauko rahoto, Harkokin Addini
31. Shafa’atu Ahmad (Londonbe), Babban mai dauko rahoto, Raya karkara
32. Kabiru Nadabo Mai Rice, Mai dauko rahoto, Raya karkara
33. Jameelat Meemi Koki, Babban mai dauko rahoto, Harkoki na musamman
34. Muhammad Wasilu Kawo, Mai dauko rahoto, Harkoki na musamman
35. Nasiru Kassim Fulatan, Babban mai dauko rahoto, Kimiyya da Fasaha
36. Kamila Muhammad Siba, Mai dauko rahoto, Kimiyya da Fasaha
37. Ibrahim Rabi’u, Babban mai dauko rahoto, Sufuri
38. Yasir Ibrahim (Monday), Mai dauko rahoto, Sufuri
39. Auwalu Sani Rogo, Babban mai dauko rahoto, Sha’anin ruwa
40. Abu Sufyan Doguwa, Mai dauko rahoto, Sha’anin ruwa
41. Fauziyya Isyaku, Babban mai dauko rahoto, Harkoin mata
42. Nabeel Sunusi, Mai dauko rahoto, Harkoin mata
43. Gambo Galadanci, Babban mai dauko rahoto, Ayyuka da Gidaje
44. Khamis B. Ayagi, Mai dauko rahoto, Ayyuka da Gidaje
Gwamna Abba ya ba mutm 100 mukami
Dazu an ji labari cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da karin nadin mukamai sama da 100 daga jiya zuwa yau a karkashin gwamnatinsa.
Gwamnan jihar ya nada wadanda za su rika taimakawa wajen yada labarai da hulda da jama’a da kuma wadanda za su taya Gwamna aiki a wasu wuraren.
Asali: Legit.ng