Cikakken Jeri: Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nadin Mukamai Fiye da 100 Cikin Awa 48
- A safiyar Asabar, 2 ga Satumba 2023, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sanar da karin wasu nade-nade
- Gwamnan Kano ya nada masu bada shawara na musamman da wasu wadanda za su rika taimaka masa
- A baya Abba Gida Gida ya na da hadimai akalla 97, da karin 111 da aka samu, adadinsu zai kai 208
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar da nadin mukamai shafinsa na Facebook.
Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce kafin yanzu majalisar dokokin Kano ta bada damar nada masu ba Mai girma gwamna shawara.
Masu bada shawarar za su yi aiki wajen kawo tsare-tsaren cigaban al’umma, masana’antu, mula da magoya baya da harkokin cikin gida.
Akwai masu bada shawara a kan dabarun siyasa, samar da abinci, sha’anin mata, tsarin Lafiya Jari, harkokin dalibai da wayar da kan jama’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Dr. Danyaro Ali Yakasai
2. Alh. Garba Aliyu Hungu
3. Dr. Bashir Abdu Muzakkari Fagge
4. Hon. Ismail Shehu Gurjiya
5. Hon. Nasiru Kunya
6. Hon. Ali Yahuza Gano
7. Hajiya Habiba Mustapha Baura
8. Hajiya (Dr.) Fatima Abubakar Amneef
9. Hon. Yusuf Shehu Kibiya
10. Hon. Ali Abdu Doguwa
11. Hajiya Aisha Muhammad Idris
12. Hon. Shehu Aliyu Yammedi
13. Comrade Nura Iro Ma'aji
14. Dr. Abdulhadi Zubairu Chula
Abba ya nada SSA 57 a tashi daya
Abba Kabir Yusuf ya amince da karin manyan hadimai na SSA da za su yi aiki a bangarori dabam-dabam domin taimakawa gwamnatinsa.
Dawakin Tofa ya ce an nada manyan masu taimakawa kan sha’anin addini, yada labarai, hulda da jama’a, fasahar ICT da kuma daukar hoto.
A jiyan ne aka nada masu taimakawa a kan makarantun gyaran hali, kafofin sadarwa na zamani, ayyuka, kungiyoyin NGOs da sauransu.
1. Anas Abba Dala
2. Ali Muhammad Bichi,
3. Alhajiji Nagoda
4. Babban Alhaji Sagagi
5. Ibrahim Muazzam Sanata
6. Ismail Murtala Zawa'i
7. Shamsu Aliyu Samanja
8. Fahad Balarabe Adaji
9. Abdullahi Ibrahim
10. Hassan Sani Tukur
11. Hadiza Aminu
12. Hon. Nasiru Isa Dikko
13. Ali Hamisu Indabawa
14. Nafi'u Dankura Adamu
15. Abdurrashid Muhammad Panda
16. Nasiru Hassan Yan Awaki
17. Abubakar Muhammad Inuwa
18. Ibrahim Ma'aji Sumaila
19. Abdullahi Ghali Basaf
20. Bashari A. Yaro
21. Habibu Ya'u Kwankwaso
22. Yusuf Abdullahi Yanoko
23. Saminu Balago Yakasai
24. Abdussalam Muhammad Sani
25. Bala Abubakar
26. Ishaq Abdul
27. Tijjani Kaura Goje
28. Balarabe Isa Abdullahi
29. Mansur Ali Galadanchi
30. Mustapha Ibrahim Chigari
31. Sani Rabi’u Muhammad (Rio)
32. Ibrahim Abdu Hanga
33. Musbahu Shado
34. Abdullahi Sabo Abubakar
35. Zainab Ibrahim D.
36. Dahiru Arrow Dakata
37. Jamilu Yamadawa
38. Yassir Abdullahi Jobe
39. Mubarak Muhammad Usman
40. Bashir Usman Gama
41. Mahmoud Abbas Sunusi
42. Adamu Maitama
43. Rabi Hotoro
44. Arc. Ahmad Ishaq
45. Arc. Abba Garba Yaro
46. Idris Tela Dandalama
47. Isa Rabi’u Wise
48. Sharu Na Malam Dandago
49. Rabiu Salisu Babba Dala
50. Aminu Sulaiman Gaya
51. Hassana Abubakar
52. Hajiya Mariya Sani Karaye
53. Hajiya Sa'adatu Salisu Yusha'u
54. Dr. Harisu Tsanyawa
55. Sani Isa Romi
56. Inuwa Salisu Sharada, (KOSSAP)
57. Khalil Isa Dokadawa (Amana Luxury)
Baya ga haka, mu na da labari Abba Kabir Yusuf ya bada mukaman SR da SSR domin a samu wakilai masu dauko rahotanni a ma’aikatu.
Abba Gida Gida ya yi hakan ne domin ya jawo matasa cikin gwamnatinsu ta NNPP ganin gudumuwar da aka ba su a lokacin yakin zabe.
Asali: Legit.ng