Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Karin Jiga-Jigai Sama da 20 a Jihar Osun

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Karin Jiga-Jigai Sama da 20 a Jihar Osun

  • Jam'iyyar APC ta dakatar da ƙarin mambobi 26 a jihar Osun bayan korar wasu sama da 80 bisa zargin cin mana
  • Shugaban APC reshen Osun, Sooko Lawal, shi ya bayyana haka a wata sanarwa, ya ce matakin yana da wahala amma ya zama dole
  • APC na fama da rikicin cikin gida a jihar tun kafin zaben gwamna wanda ta sha kaye hannun Ademola Adeleke na PDP

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Osun state - Jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta sanar da dakatar da ƙarin mambobinta kuma jiga-jigai 26 bisa zargin zagon ƙasa da cin amanar jam'iyya.

Wannan dai ya biyo bayan ƙorar da jam'iyyar APC ta yi wa wasu mambobi 84 bisa zargin cin amana a ranar Laraba da ta shige, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Jam'iyyar APC ta dakatar da mambobi 26 a Osun.
Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Karin Jiga-Jigai Sama da 20 a Jihar Osun Hoto: punchng
Asali: UGC

Shugaban APC a jihar, Mista Sooko Lawal, shi ne ya tabbatar da dakatar da ƙarin mambobi 26 a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, 2023.

Kara karanta wannan

Wike: Hadimin Atiku Ya Fadi Lokacin Da PDP Za Ta Kori Ministan Abuja

Lawal ya ce dakatarwan ta biyo bayan korafe-korafe da kuma zargin raba kan jam’iyyar da aka yi wa mambobin da abin ya shafa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton jaridar Guardian, shugaban APC na Osun ya ce:

“Bayan korafe-korafen ayyukan cin amana, kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC reshen jihar Osun ya kafa kwamitin ladabtarwa da zai binciki zargin da ake yi wa wasu mambobi."
“Kwamitin ladabtarwa ya yi bincike sosai ba tare da nuna son kai ba kan zargin kuma kwamitin zartarwa na Jiha ya yi nazari sosai kan rahoton binciken da aka kai masa."
"Bayan tantance kwararan shaidu da kuma yin la'akari da shawarwarin kwamitin, kwamitin zartarwa na jihar ya dauki mataki mai wahala, amma ya zama dole."

Jerin sunayen mambobin da APC ta dakatar a Osun

Mambobin da APC ta dakatar sun haɗa da, Alhaji Moshood Adeoti, Najeem Salami, Sanata Mudasiru Hussain, Adelowo Adebiyi, Adelani Baderinwa, Sikiru Ayedun, Kazeem Salami, Alhaji Adesiji Azeez, da Gbenga Akano.

Kara karanta wannan

Ganduje Na Yiwa APC Wankan Tsarki, An Kori Na Hannun Daman Tsohon Minista Aregbesola Su 84

Sauran sun ƙunshi, Kunle Ige, Mista Biodun Agboola, Gbenga Awosode, Rasheed Opatola, Gbenga Ogunkanmi, Israel Oyekunle, MBO Ibraheem, Akeem Olaoye, Francis Famurewa da Mista Tajudeen Famuyide.

Sai kuma Misis Adenike Abioye, Wasiu Adebayo, Rasheed Afolabi, Mista Segun Olanibi, Mista Tunde Ajilore, Mista Ganiyu Ismaila Opeyemi, da kuma Zakariah Khalid-Olaoluwa, The Cable ta tattaro.

Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Shirin Samar da Attajirai 150

A wani rahoton mun kawo muku cewa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana shirinsa na samar da Attajiran masu kuɗi 150.

Namadi ya sanar da haka ne a wurin taron raba tallafin dogaro da kai ga mata 1,000 wanda ma'aikatar mata ta jihar ta shirya ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262