Villa, Barikin Soji: Hadimin Atiku Ya Lissafo Gine-ginen Da Ya Kamata Wike Ya Rushe, Babu Su a Tsarin Abuja
- An bai wa ministan babban birnin tarayya Abuja jerin gine-ginen da ya kamata ya rushe
- An buƙaci ministan ya rushe fadar shugaban ƙasa da kuma barikokin soji da ke birnin na Abuja
- Hadimin Atiku Daniel Bwala ne ya yi wannan kiran, inda ya ce gine-ginen babu su a cikin tsarin birnin
FCT, Abuja - Daniel Bwala, mai magana da yawun Atiku Abubakar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, ya lissafawa ministan babban birnin tarayya (FCT) Abuja, Nyesom Wike wuraren da ya kamata ya rushe.
Ya ce dole ne a rushe gine-ginen idan har da gaske Wike yana son mayar da Abuja kan tsarin da take.
Fadar shugaban ƙasa Villa ba ta cikin tsarin Abuja
A yayin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, Bwala ya ce fadar shugaban ƙasa wato Villa, barikokin soji da kuma kaso 62% na rukunin gidaje, babu su a tsarin birnin na tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ƙara da cewa da yawa daga wuraren da aka bai wa sojoji an tanade su ne domin gina wuraren da jama'a za su riƙa shaƙatawa.
A cikin bidiyon da wani mai suna @uc_andrew ya ɗora a shafinsa na TikTok, Bwala ya ce ofisoshi da sauran gine-gine da aka yi a Asokoro ma duk babu su a cikin tsarin birnin tarayya.
Dan kasuwa ya sha alwashin maka Wike a kotu
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan iƙirarin da wani fitaccen ɗan kasuwa, Mohammed Ibrahim Kamba ya yi na cewa zai maka ministan Abuja Nyesom Wike a kotu.
Hakan ya biyo bayan rushe ma sa gini da Wike ya yi, wanda a cewar Ibrahim Kamba bai saɓa ƙa'idar da ake magana ba.
Ya sha alwashin cewa sai ya tura ministan zuwa gidan yarin tunda dai ya tsallake iyaka ya shigo ma sa gona.
Hadimin Atiku ya fadi matakin da PDP za ta ɗauka kan Wike
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan matakin da Daniel Bwala, wato hadimin Atiku ya ce jam'iyyar PDP za ta ɗauka a kan ministan birnin tarayya Nyesom Wike.
Bwala ya ce ba wai dakatar da Wike kawai za a yi ba, za su sallame shi ne kwata-kwata daga jam'iyyar.
Asali: Legit.ng