Shugaba Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Tsohon Gwamnan Zamfara Yari a Villa
- Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban gwamnonin Najeriya, Sanata Abdul'aziz Yari a Aso Villa
- Bayan ganawar, Sanata Yari ya bayyana muhimman batutuwan da suka sa ya ziyarci shugaban ƙasa ranar Alhamis
- Ya ce tuni gwamnatin jam'iyyar APC ta fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2027 da yadda zata sake samun nasara
FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul'Aziz Yari, ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sanata Yari, tsohon shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ya shaida wa masu ɗauko rahoton gidan gwamnati cewa tuni gwamnatin Tinubu ta fara shirin zaben 2027.
Ya kuma ce shugaba Tinubu ba shi da dalilin yin korafi saboda shi ya nemi a zabe shi a matsayin shugaban kasa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Sanata Yari mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, ya ce babu wata gwamnati da za ta so ta bar mulki ba tare da jam’iyyarta ta yi nasarar gaje ta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya ce:
"Kamar yadda kuka sani, idan zabe ya kare, shirye-shirye da tsare-tsaren da gwamnati ta ɗauko ba komai bane illa na tunkarar zaɓe na gaba."
"Babu gwamnati da zata so rashin nasara kuma ba bu gwamnatin da zata so wa'adinta ya ƙare ba tare da ta samar da wanda zai gaje ta ba, wanda ya fito daga jam'iyya ɗaya da ita.
Menene dalilin ganawarsa da Bola Tinubu?
Sanata Yari ya bayyana cewa ya je fadar shugaban kasa ne domin karfafa wa shugaba Tinubu gwiwa dangane da kyawawan ayyukan da ya fara.
A rahoton Daily Trust, Yari ya ci gaba da cewa:
“Abinda ya kawo ni, na farko na taya shi murna, da kuma karfafa masa gwiwa kan ayyukan da ya fara. Ba abu ne mai sauƙi ba, ayyuka ne masu wuyan gaske, ya dace a maida hankali da azama domin Nijeriya babbar ƙasa ce."
“Amma kamar yadda ya fada a baya, ba shi da dalilin yin korafi saboda ya nemi a zaɓe shi ya yi aikin. Mun san akwai kalubale da yawa kuma suna zuwa daga lokaci zuwa lokaci."
Tsoffin 'Yan Takardar Shugaban Kasa Sun Roki Tinubu Mukaman Gwamnati
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Yayin ganawa da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje, wasu 'yan takarar shugaban kasa sun roki mukamai.
Sun bayyana cewa sun ki shiga shari'ar zaben shugaban kasa ne saboda kishin kasa tare da barin Shugaba Tinubu mai da hankali a kan ayyukan raya kasa.
Asali: Legit.ng