Wike Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan Kotu Ta Kwace Nasarar Shugaba Tinubu

Wike Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan Kotu Ta Kwace Nasarar Shugaba Tinubu

  • Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya miƙa lamuransa ga ubangiji dangane da ƙarar da ake yi kan Shugaba Tinubu a kotun zaɓe
  • Wike ya bayyana cewa bai taɓa rashin nasara ba sannan ya yi amanna cewa ubangijin da ya ke bautawa, ba zai bari ya kunyata ba
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana amannarsa kan cewa tabbas ubangiji ba zai bari ya yi rashin nasara ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa ubangijin da ya ke bautawa ba zai bari ya yi rashin nasara ba.

A yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, tsohon gwamnan jihar Rivers ya bayyana yadda ya ke ji dangane da zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bayyana Abu 1 Da Dole Sai PDP Ta Yi Kafin Ya Mara Mata Baya a Zaben Jihar Bayelsa

Wike ya magantu kan shirinsa na gaba
Wike yana fatan kotu ba za ta kwace nasarar Tinubu ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike ya bayyana cewa yana matuƙar farin ciki cewa ya tsaya bayan gaskiya da adalci a lokacin zaɓen shugaban ƙasar wanda Shugaba Tinubu ya lashe.

Wike: "Ubangiji ba zai bari na yi rashin nasara ba"

Da aka tambaye shi ko menene abin da zai yi idan aka ce kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ƙwace nasarar Shugaba Tinubu, Wike sai ya ka da baki ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ɓan taɓa yin rashin nasara ba. Na yi amanna sosai cewa ubangijin da na ke bautawa ba ya barci."
"Na yi amanna cewa tun da ubangiji ya bari mu ka tsallake waɗannan matakan, ba zai bari mu sha wuya daga baya haka kawai ba."

"Na yi mamaki Tinubu ya bani minista", Wike

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana cewa naɗinsa ba abu ne da ya sa rai ba.

Kara karanta wannan

Ahaf: Wike Ya Sake Takalar Fada Tsakaninsa Da Atiku, PDP Ya Kalubalancesu Abu 1

Ministan na birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa ya yi mamaki lokacin da ya samu labarin nadin nasa a matsayin ministan Abuja. Wike yana ɗaya daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu ya rantsar.

Wike Ya Takali PDP Fada

A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya sake takalar jam'iyyar PDP faɗa.

Ministan na birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa jam'iyyar ta yi kaɗan ta dakatar da shi ko ta ɗauki wani matakin ladabtarwa a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng