Gwamnatin Jihar Delta Ta Magantu Kan Batun Soke Zaben Gwamna Sheriff Oborevwori

Gwamnatin Jihar Delta Ta Magantu Kan Batun Soke Zaben Gwamna Sheriff Oborevwori

  • Gwamnatin jihar Delta ta fito fili ta yi magana kan rahotannin da ke yawo cewa kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓen gwamna Sheriff Oborevwori
  • Gwamnatin jihar ta bayyana rahotannin ƙarya wanda ƴan adawa suka zauna suka shirya kuma su ke yaɗa wa
  • Gwamnatin ta bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙarar kawai ta bayar da umarnin a saurari ƙarar ɗan takarar jam'iyyar Labour Party ne

Jihar Delta - Gwamnatin jihar Delta a ranar Alhamis, ta ƙaryata labaran da ke yawo cewa kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓen gwamna Sheriff Oborevwori, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ba ta soke zaɓen gwamna Oborevwori ba, kamar yadda ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar Labour Party (LP), Mista Ken Pela, ya ke yayatawa ba.

Kara karanta wannan

Kansiloli Sun Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Zargi Gwamna Da Karkatar Da Kudade

Gwamnatin jihar Delta ta yi martani kan kwace kujerar gwamna Sheriff
Gwamnatin jihar Delta ta musanta batun kwace nasarar gwamna Sheriff Oborevwori Hoto: Dr Sheriff Oborevwori
Asali: Facebook

Da yake magana kan lamarin, kakakin watsa labaran gwamnan, Festus Ahon, ya bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙarar kawai ta bayar da umarni ne ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar, ta saurari ƙarar da Pela ya shigar.

Kotu ba ta ƙwace nasarar Oberevwori ba

Ahon a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun samu rahotanni daga wasu kafafen watsa labarai cewa kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana Mista Ken Pela na jam'iyyar Labour Party a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Delta na shekarar 2023."
"Rahotannin ba komai ba ne face ƙanzon kurege, domin kotun ɗaukaka ƙarar kawai ta bayar da umarni ne ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna da ta saurari ƙarar Mista Pela."
"Daga sakamakon da hukumar zaɓe ta INEC ta fitar, a bayyane ya ke cewa ɗan takarar Labour Party bai yi nasara ba a zaɓen, saboda haka babu yadda za a yi ya yi nasara a kotu."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Zata Ɗauki Sabbin Ma'aikata 300,000 a Faɗin Najeriya, Sahihan Bayanai Sun Fito

Festus ya kuma buƙaci al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu sannan su yi watsi da rahotannin domin ƙarya ce tsagwaronta wacce ta fito daga jam'iyyar Labour Party da mabiyanta.

Ya kuma bayyan cewa lauyoyinsu na yin duba kan hukuncin kotun domin sanin matakin da za su ɗauka na gaba.

Wike Ya Shawarci Jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya shawarci jam'iyyar PDP kan abin da za ta yi idan tana son ya yi mata aiki a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa

Wike ya bayyana cewa dole sai jam'iyyar ta nemi afuwarsa da ta takwarorinsa kafin ya duba yiwuwar yi mata aiki a zaɓen gwamnan da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng