Ganduje Na Yiwa APC Wankan Tsarki, An Kori Na Hannun Daman Tsohon Minista Aregbesola Su 84

Ganduje Na Yiwa APC Wankan Tsarki, An Kori Na Hannun Daman Tsohon Minista Aregbesola Su 84

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun ta sanar da korar 'ya'yanta 84
  • Jam'iyyar mai mulki ta zargi mambobin nata 84 da aka kora da cin dunduniyar jam'iyya a jihar
  • Mambobin APC din da aka sallama sun kasance masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Osogbo, Jihar Osun - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Osun ta kori mambobinta 84 wadanda ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola.

Shugaban APC a Osun, Sooko Lawal, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, jaridar PM News ta rahoto.

APC ta fatattaki 'ya'yanta 84 a jihar Osun
Tashin Hankali Yayin da APC Ta Kori ‘Ya’yanta 84 Masu Biyayya Ga Tsohon Gwama Aregbesola, Ta Fadi Dalili Hoto: Rauf Aregbesola
Asali: Facebook

Dalilin da yasa APC ta kori masu biyayya ga Aregbesola

A cewar sanarwar, ana zargin masu biyayya ga Aregbesola 84 da cin dunduniyar jam'iyya.

Kara karanta wannan

Ana Dakon Hukuncin Kotu Kan Zaben Abba, Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan matakin ladabtarwan ya zo ne a matsayin martani ga zarge-zargen da ake yi masu na rashin da'a da ayyukan da suka kunyata jam'iyyar.
"Kwamitin ladabtarwa ya gudanar da bincike sosai kan zarge-zargen kuma kwamitin zartarwa na jihar ya yi nazari da kyau a kan abubuwan da aka gano.
"Bayan cikakken nazari kan hujjar da la'akari da shawarwarin kwamitin, kwamitin zartarwa na jihar ya dauki matakin mai wahala amma wanda ya dace na korarsu..."

Legit.ng ta fahimci cewa lamarin na zuwa ne bayan tsohon ministan harkokin cikin gida, Aregbesola ya kaddamar da jiga-jigan APC Omoluabi a Osun a ranar Talata, 22 ga watan Agusta.

A yayin bikin kaddamarwar, Aregbesola ya yi korafin cewa masu ruwa da tsaki na Omoluabi sune ainahin wadanda suka kafa APC a Osun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Kara Haddasa Ruɗani a PDP Kan Ministan Shugaba Tinubu

Tsohon ministan ya ce an kaddamar da yan Omoluabi ne don sabonta hanyarsu a ci gaban siyasa kamar yadda suka gada daga Cif Obafemi Awolowo, da Cif Bola Ige da sauransu.

Ya bayyana cewa za a iya gano dalilin kayen da APC ta sha a jihar Osun da wannan manufofin na ci gaba.

Jerin jiga-jigan PDP da Tinubu ya nada mukami

A wani labarin, mun ji cewa jim kadan bayan nasarar Shugaban Kasa Bola Tinubu a babban zaben 2023, ana ta rade-radin cewa yana shirin kafa gwamnati ta hadin kan kasa ta hanyar nada wasu yan siyasa masu adawa mukamai.

Daga baya shugaban kasar ya ce ya fi sha'awar kafa gwamnati da za ta yi aiki don gina kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng